N'Golo Kante: Chelsea ta hana dan wasan zuwa atisaye saboda fargabar coronavirus

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Daga Alistair Magowan
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sport
Chelsea za ta bar N'Golo Kante ya kauracewa atisaye saboda fargabar kamuwa da cutar korona - ko da kuwa hakan na nufin ba zai buga wasa ba har karshen kakar bana.
Dan wasan tsakiyar na Faransa, mai shekara 29, ya koma yin takaitaccen atisaye ranar Talata a filin wasan kungiyar da ke Cobham.
Sai dai tuni ya yanke shawarar yin atisaye a gida, matakin da Chelsea ta amince da shi.
Kante ya sanya fargaba a zukatan abokan wasansa a 2018 lokacin da ya suma ana tsaka da atisaye; a shekarar ce kuma dan uwansa ya rasu sakamakon bugun zuciya.
Alkaluman da Hukumar Dididdiga ta Burtaniya ta fitar sun nuna cewa bakaken mutane da mata sun fi yiwuwar kamuwa da cutar korona sau biyu idan aka kwatanta da fararen mutane a Ingila da Wales.
Matakin da Kante ya dauka ya zo daidai da wanda Watford captain Troy Deeney ya dauka.
Ranar Talata an tabbatar cewa mutum shida ne suka kamu da cutar korona a kungiyoyi uku na Gasar Premier, cikinsu har da dan wasan Watford Adrian Mariappa.







