Kotu ta tilasta wa kaka goge hotunan jikokinta da ta sa a Facebook

A woman on a smartphone

Asalin hoton, Getty Images

Wata kotu a ƙasar Netherlands ta yanke hukuncin cewa wata mata ta goge hotunan jikokinta da ta wallafa a shafukan sada zumunta na Fesbuk da Pinterest ba tare da izinin mahaifansu ba.

Lamarin ya kai ga kotu ne bayan matar ta samu saɓani da 'yarta.

Kotun ta yanke hukuncin cewa batun yana cikin iyakar Ƙa'idar Kare Bayanai ta Tarayyar Turai (EU's General Data Protection Regulation).

Wani ƙwararre ya ce hukuncin manuniya ce kan "matsayin da Kotun Turai ta ɗauka tsawon shekaru game da kare bayanan mutum".

Maganar ta je gaban kotu ne bayan matar ta ƙi goge hotunan jikokinta da ta wallafa a shafukan sada zumunta.

Mahaifiyar yaran ta yi ta neman a goge hotunan 'ya'yan nata, amma kakarsu ta yi ƙememe.

Tana iƙirarin cewa Ƙa'idojin Kare Bayanai ba sa aiki kan abin da yake na "tsagwaron raɗin-kai" ko kuma "amfanin gida" ne wajen sarrafa bayanan mutum.

Sai dai, wannan togaciya ba ta aiki don kuwa wallafa hotuna a shafukan sada zumunta ya sa wasu dumbin mutane na iya samunsu, cewar hukuncin.

"Ta hanyar Fesbuk, ba za a iya kauce wa yaɗa hotunan da aka wallafa ba kuma suna ma iya ƙarewa a hannun wasu 'yan kiɗanka-na-jiyo," in ji kotu.

Jazaman ne sai matar ta cire hotunan ko ta biya tarar yuro hamsin kwatankwacin naira 21,000 kullum da ranar Allah Ta'ala da ta ƙi biyayya da umarnin, har zuwa mafi tsanani a ci ta tarar yuro 1,000.

Facebook logo

Asalin hoton, Reuters

Idan kuma ta sake wallafa hotunan yaran a nan gaba, kotu za ta sake cin ta tarar ƙarin yuro hamsin a kullum.

Wani lauya kan ayyukan ƙere-ƙere, Neil Brown ya ce "Ina jin hukuncin zai bai wa ɗumbin mutane mamaki waɗanda mai yiwuwa ba sa zurfafa tunani kafin su wallafa saƙon tiwita ko kuma su buga hotuna".

"Ko ma ba matsayin doka, shin ba zai fi hankali ba ga mutanen da ke wallafa irin waɗannan hotuna su yi tunani, 'Anya, ƙila wanda ko wadda zan sa hotonsa ko nata, ba zai so haka ba".