Kotun Ƙoli ta soke hukuncin ɗaure Orji Kalu, amma EFCC ta ce tana da ja

Kotun Ƙolin Najeriya ta soke hukuncin ɗaurin shekara 12 a gidan yari da aka yanke wa tsohon gwamnan jihar Abia, Orji Uzor Kalu.
Kotun Kolin, wacce ta soke hukuncin ranar Juma'a, ta ƙara da cewa alƙalin da ya yanke hukuncin ba shi da hurumin yi wa tsohon gwamnan shari'a.
A cewarta, lokacin da Mai Shari'a Mohammed Idris na kotun tarayya da ke Legas ya yanke hukuncin, an riga an daga likafarsa zuwa matsayin alƙalin Kotun Ɗaukaka Ƙara ta ƙasar, don haka ba shi da hurumin yanke hukunci kan shari'ar ta Mr Kalu.
A shekarar 2019 ne Mai Shari'a Idris ya yanke wa Mr Kalu hukuncin ɗaurin shekara 12 a gidan yari.
Hakan ya faru ne bayan kotun ta tabbatar da zargin da ake yi masa tare da wasu mutum biyu kan almundahanar naira biliyan 7.65.
Lamarin ya faru tun lokacin Mista Kalu yana gwamnan jihar Abia inda daga baya ya koma Majalisar Dattawa a matsayin Sanata.
Mista Kalu dai dan jam'iyyar APC ne wadda ita ce jam'iyya mai mulki da Shugaban kasar Muhammadu Buhari yake a cikinta.
Ba a cika samun kotu na yanke wa 'yan siyasa irin wannan hukuncin da aka yanke wa Mista Kalu ba a kasar, duk da cewa ba sabon abu ba ne, ya faru da wasu tsofaffin gwamnoni.
'Za mu koma fagen daga'
A martanin da ya yi bayan hukuncin Kotun, tsohon gwamnan ya gode wa Kotun Ƙolin inda ya ce ta yi masa adalci.
"Kotun Ƙolin ƙasarmu ta tabbatar da 'yancina na damar ji daga bakina da kuma kariya ta shari'a," a cewar Mr Kalu.
Sai dai hukumar EFCC da ke yaƙi da masu yi wa tatalin arzikin Najeriya ta'annati ta yi allawadai da hukuncin sannan ta ce za ta koma fagen daga don ganin an hukunta tsohon gwamnan.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
A sakon da ta wallafa a Twitter, hukumar ta ce "EFCC tana kallon hukuncin da Kotun Ƙolin ta yanke a matsayin abin takaici. Wata kitimurmurar shari'a ce kawai ta kare tsohon gwamnan. Hukumar nan a shirye take a sake shigar da ƙara a kan batun ba tare da ɓata lokaci ba saboda shaidun da take da su a kan Kalu da sauran mutanen ba za a iya yin rufa-rufa a kansu ba," in ji EFCC.











