Tsofaffin gwamnonin Najeriya da aka tura gidan yari

Orji Uzor Kalu

An yanke wa tsohon gwamnan jihar Abia Orji Uzor Kalu hukuncin daurin shekara 12 a gidan yari.

Mai shari'a Mohammed Idris ne na kotun tarayya da ke Legas ya yanke wannan hukunci.

Hakan ya faru ne bayan kotun ta tabbatar da zargin da ake yi masa tare da wasu mutum biyu kan almundahanar naira biliyan 7.65.

Lamarin ya faru tun lokacin Mista Kalu yana gwamnan jihar Abia inda daga baya ya koma Majalisar Dattawa a matsayin Sanata.

Mista Kalu dai dan jam'iyyar APC ne wadda ita ce jam'iyya mai mulki da Shugaban kasar Muhammadu Buhari yake a cikinta.

Ba a cika samun kotu na yanke wa 'yan siyasa irin wannan hukuncin da aka yanke wa Mista Kalu ba a kasar, duk da cewa ba sabon abu ba ne, ya faru da wasu tsofaffin gwamnoni.

Wasu daga cikin gwamnonin da irin wannan hukuncin ya rutsa da su sun hada da;

Joshua Dariya

Jiha: Filato

Jiha: Tsohon gwamna

Hukunci: Shekaru 14 cikin gidan yari sakamakon samunsa da laifin almundahanar naira biliyan 1.6

Rana: Yunin 2018

Diepreye Alamieyeseigha (Marigayi)

Jiha: Bayelsa

Mukami: Tsohon gwamna

Hukunci: Daurin shekaru biyu a gidan yari kan laifuka shida na almundahanar kudi da suka kai biliyan 1.6

Rana: Yulin 2007

James Ibori

Jiha: Delta

Mukami: Tsohon gwamna

Hukunci: Daurin shekaru 13 a gidan yari kan laifuka 10 da suka shafi kulla makirici domin almundahana da kuma fitar da kudi ba kan ka'ida ba (dala miliyan 77)

Rana: Afrilun 2012

Jolly Nyame

Jiha: Taraba

Mukami: Tsohon gwamna

Hukunci: Shekaru 28 a gidan yari kan laifuka 41 daban-daban.

Rana: Mayun 2018