Coronavirus: Kananan sana'o'i takwas da kullen annobar ya shafa a Najeriya

Tun bayan da cutar korona ta bayyana a Najeriya, gwamnatocin wasu jihohi da ta kasa suka sanya dokar zama a gida don takaita yaduwar cutar. Dokar ta kunshi rufe dukkan masana'antu, amma ban da masu samarwa da sayar da kayan abinci da magunguna.

Dokar ta hana fita ta shafi kanana da matsakaitan masana'antu da dama a Najeriya, kuma ta janyo matsin tattalin arziki ga miliyoyin 'yan kasar da suka dogara da cinikin yau da kullum wajen ciyar da kansu da iyalansu.

Masanin tattalin arziki a Najeriya, Dakta Muhammad Shamsudeen na Jami'ar Bayero da ke Kano ya ce adadin kanana da matsakaitan masana'ntu da suka yi rajista da gwamnati sun kai miliyan 41 da rabi.

"Ban da kananan masana'antu da ba su yi rajista ba kamar masu yankan farce da masu wankin takalmi da teloli na cikin gida da dai sauransu,"a cewarsa.

Haka kuma, kusan kashi 11.5 cikin 100 na wadannan masana'antu na jihar Legas ne, babbar cibiyar kasuwanci ta Najeriya.

Dakta Shamsudeen ya ce alkaluma sun nuna cewa kanana da matsakaitan masana'antu na samar da aiki ga kusan mutum miliyan 60 a Najeriya.

Gudunmawar da kananan masana'ntu ke bayarwa ga tattalin arzikin kasa na da yawa.

"A iya cewa kusan kashi 50 cikin 100 na tattalin arzikin kasa gaba daya ya dogara ne a kan kanana da matsakaitan masana'antu da wadanda suka yi rajista da wadanda basu yi ba.

Mun duba wasu daga cikin masana'antun da suka fuskanci matsi yayin wannan kulle.

Shagunan aski da gyaran gashi na mata

Shagunan aski na maza da shagunan gyaran gashi na mata sun kasance a rufe tun da shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya sanya dokar hana fita a karshen watan Maris.

Akasari, a wadannan shaguna a kan ga cunkuson mutane masu jira a yi masu aski ko kitso ku kuma a yi masu shamfu.

Haka kuma, a irin shagunan nan a kan samu masu yin kwalliya irin ta zamani, kuma su ma sun fuskanci koma baya a sana'o'insu dalilin kullen.

Rabi Abbas Yakubu, wata mai shagon gyaran gashi da kwalliya da dinki ce a kasuwar Garki da ke Abuja kuma ta ce ba ta taba shiga halin da ta shiga ba a yanzu.

"Dole na rufe shago na tattara nawa ya nawa na bar garin saboda babu ciniki. Na koma Kaduna inda can iyayena suke," a cewarta.

"Ita harkar kwalliya dole sai an shafi juna, kuma yadda wannan cuta take ba zai yiwu in ci gaba ba."

"Ina fargabar durkushewar sana'ata gaba daya saboda wannan cuta," a cewarta.

Gidajen abinci

An rufe gidajen cin abinci gaba daya saboda wannan doka, duk da cewa wasu gidajen abincin na budewa amma ba sa bari mutane su zauna a ciki su ci, sai dai a saya a tafi.

Wasu gidajen na amfani da shafukan sada zumunta musamman Instagram wajen sayar da abincin nasu inda mutane ke saye su kuma su kai wa mutane abincin har gida, tare da biyan kudin kai wa.

Masu shirya bukukuwa

A 'yan shekarun nan, bukukuwa sun zama manyan shagulgula inda ake kama manyan dakunan taro na musamman sannan a kayata dakunan, a kira masu kide-kide da masu shela, wato M.C.

Sai dai yanzu duk wadannan ba su yiwuwa saboda dokar hana fita da aka sa.

An soke duk shagulgulan biki a yayin wannan lokaci na kulle don haka masu bayar da dakunan taro haya da masu dafe-dafen abincin biki da makida da masu shela duk ayyukansu sun tsaya cik.

Teloli da masu shagunan sayar da kayan sawa

Masu dinka kaya da masu sayar da kayan sawa na daga cikin wadanda dokar ta hana bude sana'o'insu.

Wata mai sayar da dinkakkun a Abuja mai suna Yemi ta ce ta rufe shagonta saboda kullen.

Ta ce "Yanzu dole a gida nake yin dinkin kayana, kuma babu masu saya sosai ba kamar da ba.

"Kayan da nake sayarwa naira dubu sha biyar zuwa dubu sha biyu dole na rage masu farashi. Har dubu takwas yanzu nake sayarwa don dai kawai in rabu da su," a cewarta.

Ta kuma koka kan yadda ba ta samun yadukan da take amfani da su wajen dina kayan saboda kasuwanni a rufe suke yanzu.

Ita ma Rabi Abbas Yakubu ta ce "abin tashin hankalinma shi ne sallah ta kusa yanzu. Lokacin sallah muna samun dinkuna sosai amma yanzu babu hali.

"Wasu da suka biya kudin kayansu suna so in mayar masu da kudinsu tun da ban kammala dinkin ba," in ji ta.

Shagunan sayar da kayan shafa da kayan kwalliya

Masu hadawa da sayar da mayukan gyaran jikin mata ma na cikin sana'o'in da suka fuskanci cikas a wannan lokaci na kulle.

Wata mai hada kayan gyaran jiki, Farida Ali Adamu ta shaida wa BBC cewa sana'arta na cikin tsaka mai wuya.

"Biyan kudin hayar shago ma kawai ya ishe ni jimami. Yanzu ba kayan kwalliya ne a gaban mutane ba, abin da za su ci shi ne kan gaba.

"Don haka, kwastomomina sun ragu. Sannan kayan da nake amfani da su wajen hada mayuka da sabulai yanzu sun yi wuya saboda da yawa daga kasashen waje nake shigo da su.

"Idan aka ci gaba da wannan kullen, karshenta sai dai in rufe shagona kuma in sallami ma'aikatana," in ji Farida.

Motocin haya na bas da tasi da Keke Napep da Babur

Kusan a iya cewa masu motocin haya da Babura da keke Napep na cikin wadanda dokar ta fi shafa saboda hana zirga-zirga da aka yi gaba daya.

Jami'an tsaro na sa shingaye a titi don hana masu motocin haya da babura da Keke Napep wucewa.

Kuma saboda hana fita, mutane na zaune a gidajensu babu inda suke zuwa balle su bukaci abin hawa.

'Yan Talla

Masu yawo da hajarsu a hannu kamar jaridu da mujallu da faya-fayen CD da kayan ciye-ciye kamar su alewa da cingam da gyada da kwakwa da dai sauransu na cikin wadanda wannan dokar ta shafi tattalin arzikinsu.

An haramta wa wadannan mutane yawo a tituna don sayar da kayansu, kuma saboda mutane ba sa fitowa, ba za su samu ciniki ba.

Kanikawa da masu sayar da bangarorin mota da kayan wuta

Wannan rukuni na sana'o'i sun kasance ba ciniki a wannan lokaci.

Haka ma masu sayar da kayan wutar lantarki irinsu kwan fitila da wayoyin wuta da masu sayar da kayan gini irin su sumunti da bulo duk ayyukansu sun tsaya cik.

Dakta Muhammad Shamsudeen na Jami'ar Bayero da ke Kano ya ce ko kasashen da suka ci gaba mafi yawan masan'antunsu kanana ne da matsakaita.

"A Najeriya ma haka abin yake," a cewar Dakta Shamsudeen.

Tasgaro ga kananan masana'antu

Hukumar Kididdiga ta Najeriya ta ce wadanann masana'antu na samar da aikin yi ga kimanin mutum miliyan 60 a Najeriya, kuma ana iya ganin haka a harkar noma da ayyukan hannu misali saka da rini da aski da tukin mota da sauransu.

Dakta Shamsudeen ya ce "suna sama wa gwamnati kudin shiga na haraji kuma ana fitar da wasu daga cikin kayayyakin da ake samarwa. Wannan na taimaka wa darajar tattalin arzikin kasar."

Kanana da matsakaitan masana'antu na taimaka wa kokarin gwamnatoci na fadada tattalin arziki kuma sun rage radadin talauci ga wadanda ba su samu aikin gwamnati ba.

Dakta Shamsudeen ya ce babu shakka, wannan kulle zai yi matukar shafar ayyukan kananan masana'antu.

"Mafi yawansu ba su da jari mai yawa. Idan aka duba abin da suke sayarwa a shekara gaba daya duka-duka ba sa samun a kalla miliyan 20" in ji Dakta Shamsudeen.

Ya ce babu wata kididdiga da ta nuna irin asarar da za a yi a bangaren kananan masana'antu kawo yanzu, amma duba da irin gudunmawar da suke bai wa tattalin arziki, wato kusan kashi 50 lallai za a yi asara sosai.

"Da yawansu za su yi asara. Na farko dai su kansu ba su da halin su fito su sayar da kayansu sannan masu yi masu cinikin su ma ba hali su fito. Wannan babban kalubale ne," a cewar Dakta Shamsudeen.

Sannan ya ce da yawa daga cikin wadannan masana'antu sun karbi bashi a banki don taimakawa hada-hadar kasuwancinsu.

"Sannan an hana tafiye-tafiye. Sana'o'i da dama sun dogara ne da wadannan abubuwan" in ji shi.

Wadannan abubuwan, a cewar Dakta Shamsudeen na daga cikin abubuwan da za su kawo tasgaro ga kanana da matsakaitan masana'antu kai tsaye a Najeriya.