Coronavirus: Doron kasa ya rage motsi saboda mutane da yawa na killace a gida

Lokacin karatu: Minti 3

Biliyoyin mutane a fadin duniya na killace a gida saboda annobar coronavirus - har ta kai hakan ya sauya yadda doron kasarmu ke motsi.

Saboda sabbin dokokin zama a gida, yanzu babu yawan zirga-zirga zuwa wuraren aiki da mota ko da jirgin kasa, kuma dole masana'antu da yawa suka dakatar da ayyukansu.

Asali ma, da yawanmu ba sa wani aiki sosai, shi ya sa ma motsin da saman doron kasa ke yi ya ragu. Wannan abin ban mamaki ne ganin cewa duniyarmu ta yi nauyin tan biliyan tiriliyan shida.

Motsin ya ragu matuka

Masana kimiyya a Royal Observatory a Belgium, wani wuri da ake sa ido duniyoyi da sama jannati ne suka fara lura da yadda motsin ya ragu inda suka ce motsin kasar na kan mita 1-20 Hz [ya fi sautin garaya zurfi amma yana kama da sautin wanni babban abin kida ake kira 'organ'] wato ya ragu tun da aka fara bin dokokin gwamnati na hana fita."

An lura da sauye-sauyen a wasu sassan duniya.

Masana a bangaren girgizar kasa a Nepal sun ga ragi a motsin, wani ma'aikaci a Makarantar Kimiyyar Doron Kasa da ke Paris, ya ce ragin da aka samu a babban birnin na Faransa na da matukar yawa kuma wani bincike a Jami'ar Cal Tech a Amurka ya bayyana cewa ragin da aka samu a birnin Los Angeles na da gagarumin yawa.

Ana iya ganin ragin da aka samu a motsin da kasa ke yi a Nepal a wannan zanen.

Iska mafi tsafta

Coronavirus ta sauya abubuwa da dama dangane da yadda muke rayuwa- da ma yadda duniyar take asalinta

Tauraron dan Adam ya gano raguwa a iskar gas ta nitrogen dioxide da ke gurbata iska, wadda kuma motoci da masan'antu ke fitarwa.

Wani abu kuma shi ne, duniyar ta yi lamo, babu hayaniya sosai.

Masana kimiyya da ke gwada hayaniyar da ake yi kullum a biranenmu, da masu bincike kan zurfin tekuna sun ce hayaniya ta ragu sosai.

Ana samun sakonni karara

Sabon binciken kan motsin doron kasar ba ya nufin ta daina motsi kwata-kwata, amma bambancin motsin nata na da, da na yanzu na da amfani ba wai ga masana kimiyya ba kawai.

Ayyukan dan Adam kamar wata hayaniya ce da ke sa sauraron abin da doron kasar ke yi, ya yi wahala.

"Za ka sami sako ba tare da wata hayaniya mai yawa ba yanzu, kuma wannan zai ba ka damar samun bayanai fiye da da," in ji masanin kimiyyar kasa Andy Frassetto a kan shafin bangaren binciken kasa na Incorporated Research Institutions for Seismology in Washington.

Wasu masu bincike sun iya gano takamaimai abinda ya jawo ragin motsin a yankinsu.

Stephen Hicks, wanda ke aiki a Kwalejin Imperial da ke London, y ace ragin bay a rasa nasaba da rashin motoci kan titin M4 - wani titi da ya hada birnin London da kasar Wales.

"Bisa ga dukkan alamu a 'yan kwanakin da suka wuce, karuwar da aka samu a yawan sautin doron kasa da ke fita da asuba ya fi karar da ake samu a makonnin da suka wuce," ya wallafa a Twitter.

"Ina ganin wannan ya faru ne saboda babu mutane da yawa masu gaggawar zuwa makaranta ko wuraren aiki da safe."

Sauye-sauye a yanayi

Kamar yadda za ku yi tunani, ayyukan dan Adam na bambanta ko wace rana da shekara saboda mutane sun fi kaiwa da komowa a wasu lokuta.

An fi samun saukin hayaniya da dare kuma ana samun raguwar hayaniya lokuttan hutu da manyan shagulgula.

Amma abin da ke faruwa a duniya yanzu shi ne ragi a ayyuka tsawon makonni ko ma watanni, abin da aka fi gani a lokutan bukukuwan kirsimeti a kasashen da ke da yawan mabiya addinin Kirista.