PSG ta nemi dauko Pogba, Ronaldo ba zai koma Manchester United ba

Paris St-Germain ta bukaci sayo dan wasan Manchester United da Faransa Paul Pogba, mai shekara 27 - kuma a cikin yarjejeniyar dauko shi har da bayar da dan wasan Argentina, mai shekara 32 Angel di Maria - wanda bai tabuka abin kirki ba a Old Trafford a shekarar 2015. (Mail)

Pierre-Francois, mahaifin Pierre-Emerick Aubameyang, ya bai wa dan wasan na Gabon mai shekara 20 shawarar sabunta kwantaraginsa a Arsenal a wani sakon Instagram da ya wallafa dauke da hoton dan wasan yana sanya hannu kan kwangilarsa ta farko a kungiyar. (Mirror)

Dan wasan Portugal Cristiano Ronaldo, mai shekara 35, ya sha alwashin ci gaba da zama a Juventus zuwa 2022 a yayin da ake rade radin cewa zai koma Manchester United. (Sun)

Borussia Dortmund ta yi amannar cewa za ta iya rarrashin dan wasan Ingila Jadon Sancho, mai shekara 20, ya ci gaba da zama a kungiyar duk da hasashen da ake yi cewa ya amince ya koma Manchester United. (Teamtalk)

Har yanzu shugaban Real Madrid Florentino Perez yana fatan dauko dan wasan Paris St-Germain Neymar, a cewar wakilin dan wasan mai shekara 28 dan kasar Brazil. (Goal)

PSG ta gwammace "barin Kylian Mbappe ya ci gaba da lalacewa a benchi" maimakon sayar wa Real Madrid dan wasan na Faransa mai shekara 21. (Sun)

Kocin Tottenham Jose Mourinho da kansa ya kira dan wasan PSG dan kasar Belgium Thomas Meunier, mai shekara 28, a yunkurin da yake na karfafa masu tsaron bayan kungiyar. (Express)

Dan wasan Leicester City James Maddison, mai shekara 23, ya gaya wa wani mai goyon bayansa cewa zai ci gaba da zama a kungiyar, abin da ya kawo karshen rade radin da ake yi cewa zai koma Manchester United. (Goal)

Leicester na sha'awar dauko dan wasan Lille Victory Osimhen, mai shekara 21, ko da yake kungiyoyin Italiya — Juventus da Inter Milan suna iya riga ta daukar dan wasan na Najeriya. (Mail)

Akwai bukatar Arsenal ta samu gurbin shiga gasar Zakarun Turai a kakar wasa mai zuwa idan tana son dauko dan wasan Atletico Madrid da Ghana Thomas Partey, 26. (Express)

Norwich da Danel Sinani sun amince da yarjejeniyar shekara uku da za ta kai ga dauko dan wasan na Luxembourg daga F91 Dudelange. (Sky Sports)