Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Paul Pogba: Na kosa a koma murza leda
Dan kwallon Manchester United Paul Pogba ya ce ya kosa ya koma buga kwallo saboda a kakar wasa ta bana jinya ta hana shi nuna kansa.
Dan wasan na Faransa mai shekaru 27, bai buga kwallo ba tun a ranar 26 ga watan Disambar bara saboda rauni a kafarsa.
Pogba ya shaidawa shafin United cewa "na shiga cikin damuwa na tsawon lokaci" amma zan soma horo da zarar an dage haramci da aka yi saboda annobar coronavirus.
Ya ce "Na kusa, a yanzu tunanin horo kawai nake yi."
Dan wasan wanda ya lashe gasar kofin duniya a Rasha a 2018, a cikin watan Junairu aka yi masa tiyata lamarin da ya sa sau takwas kacal ya murzawa United leda a kasar bana.