Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Manchester United za ta sayar da Paul Pogba
Kungiyar Manchester United na shirin sayar da Paul Pogba domin ta samu kudin sayo wasu 'yan wasan a badi.
United za ta yi amfani da kudin da ta sayar da Pogba, domin taya wasu 'yan kwallon da ta ke son yin zawarci a badi.
Jaridar Mirror ta ce United din za ta yi zawarcin Raphael Varane mai tsaron bayan Real Madrid da Toni Kross dan kwallon tawagar Jamus.
Haka kuma jaridar ta ce United din za ta tuntubi mai tsaron bayan Paris St-Germain, Marquinho da Marco Verratti dan kwallon tawagar Italiya da kuma Alex Sandro mai tsaron bayan Juventus.
Pogba ya buga wa United wasa 19, ya kuma ci kwallo uku, inda United ta ci wasa 13 da ya buga aka doke ta a biyu a kakar bana.
United tana ta biyu a kan teburin Premier, za kuma ta buga wasan daf da karshe da Tottenham a Gasar Cin Kofin FA a cikin watan Afirilu a Wembley.