Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Masu cutar coronavirus sun kai 27 a Kano
Adadin mutanen da suka kamu da cutar korona kawo yanzu ya kai 27 a Kano, bayan da aka sanar da karin mutum 5 da suka harbu da cutar a daren Juma'a.
Kano dai a yanzu ita ce ta uku wajen yawan wadanda suka kamu da cutar a Najeriya, baya ga Legas da Abuja, kuma har ma ta yi sanadin mutuwar mutum guda a ranar Laraba.
A sakon da ta wallafa a shafinta na Twitter, hukumar dakile cututtuka masu yaduwa ta kasa ta ce ya zuwa karfe 10:10 na daren Juma'a, "adadin masu dauke da cutar a Najeriya kai 493 inda Kano ke da 27."
Wannan adadi na zuwa ne kasa da mako guda da samun bular cutar karo na farko a Jihar.
A wannan juma'ar aka sanar da cewa shugaban kwamitin da ke yaki da cutar a Kano ya kamu da cutar kamar yadda ma'aikatar lafiyar jihar ta sanar.
A ranar Asabar ne kuma hukumomi suka sanar da manema labarai cewar wani mutum ya kasance na farko wanda ya kamu da cutar a jihar.
Bayanan da hukumomi suka fitar sun nuna cewa mutumin, wanda yake zaune a karamar hukumar Tarauni, ya baro Abuja inda ya isa Kano a jajibirin ranar da za a rufe hanyoyin shiga jihar.
Gwamnatin jihar ta Kano ta yi feshin magani a wurare biyar da mutumin ya kai ziyara kafin a gano yana dauke da cutar.
A hirarsa da BBC kan bullar cutar coronavirus a Kano, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya ce za a dauki tsauraran matakai domin kare al'ummar jihar.
Daga cikin matakan, Gwamnan ya haramta wa 'A daidaita sahu daukar mutum fiye da daya', ko da yake daga bisani an amince a rka daukar mutum biyu.
Su ma motocin haya, an hana su daukar mutane fiye da kima.
Kazalika, gwamnatin jihar ta ce za ta dauki matakai na rufe wasu kasuwanni tana mai cewa za a bar kasuwannin da ke sayar da kayan abinci da sauran kayan bukatar gaggawa su ci gaba da budewa.
Da ma tuni aka samu bullar cutar a jihohin da ke makwabtaka da Kano, wato Kaduna da Katsina.
Hukumar da ke dakile cututtuka masu yaduwa NCDC ta ce ya zuwa Talata da maraice ta tabbatar da cewa mutum 373 ne suka kamu da cutar, 99 suka warke yayin da 11 suka mutu a fadin kasar.
Karin labarai masu alaka: