An yi feshin magani a wuraren da mai coronavirus ya ziyarta a Kano

Gwamnatin jihar Kano da ke Najeriya ta yi feshin magani a wurare biyar da mutumim da aka tabbatar yana dauke da coronavirus ya kai ziyara kafin a gano yana dauke da cutar.

Kwamishinan Muhalli na jihar, Dr Kabiru Ibrahim Getso ne ya jagoranci ma'aikatansa wurin yin feshin.

An yi feshin ne a Masallacin Juma'a na Da'awah da Masallacin Juma'a na Dan Adalan Kano da cibiyar gwajin cututtuka ta Providian Diagonistic da ta FAN Diagonistic, da asibitin Prime Specialist da kuma gidan mutumin.

An kulle dukkan wuraren kuma gwamnati za ta ci gaba da yi musu feshi, a cewar kwamishinan.

A ranar Asabar ne hukumomi suka sanar da manema labarai cewar wani mutum ya kasance na farko wanda ya kamu da cutar a jihar.

Bayanan da hukumomi suka fitar sun nuna cewa mutumin, wanda yake zaune a karamar hukumar Tarauni, ya baro Abuja inda ya isa Kano a jajiberen ranar da za a rufe hanyoyin shiga jihar.

A jawabinsa na musamman ga al'ummar jihar kan bullar cutar coronavirus a Kano, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya ce za a dauki tsauraran matakai domin kare al'umman jihar.

Daga cikin matakan, Gwamnan ya haramta wa babur mai kafa uku wanda aka fi sani 'A daidaita sahu' daukar mutum fiye da daya.

Kazalika za a rufe wasu kasuwanni da ba na kayan abinci ba ne.

Da ma tuni aka samu bullar cutar a jihohin da ke makwabtaka da Kano, wato Kaduna da Katsina.