Coronavirus: Uwa da ‘ya’yanta sun kamu da cutar a Jihar Katsina

Karin mutum uku sun kamu da cutar coronavirus a Jihar Katsina, a cewar Gwamnan Jihar Aminu Bello Masari.

Gwamnan ya ce mutum ukun da suka kamu iyalan likitan nan ne da ya mutu a garin Daura sakamakon cutar - matarsa daya da yara biyu.

Kazalika an saka dokar hana fita a garin na Daura. Wadanda suka kamu da cutar a Jihar Katsina sun zama hudu kenan, dukkaninsu a garin Daura.

Tun a ranar Talata ne Gwamna Masari ya tabbatar wa BBC da mutuwar likitan, wanda ya ce ya kamu da cutar ne a Jihar Legas.

Babban sakatare a ma'aikatar lafiya ta jihar, Dr Kabir Mustafa ya ce tuni aka killace mutum hudu a asibitin da likitan ya rasu.

Gwamna Masari ya ce: "Duk da cewa ana ci gaba da bin sawu da kuma gwada jinin mutane a Daura, an saka dokar hana fita a garin, wadda za ta fara aiki da karfe 7:00 na yammacin gobe [Asabar]."

Amma za a zabi wasu kantunan sayar da magunguna da kuma wurin cefanen kayan abinci uku-uku wadanda mutane za su rika zuwa cikin tsauraran matakan sa ido, a cewar gwamnan.

Har wa yau, gwamnatin Katsina za ta tallafa wa mutanen Daura a lokacin da wannan doka za ta yi aiki.