Coronavirus: Yadda ta bulla a garin Daura har ta kashe likita

Latsa alamar lasifika da ke sama domin sauraron hira da Gwamna Masari:

Hukumomin kiwon lafiya a jihar Katsina sun ce sun dukufa wajen gano mutanen da likitan da ya mutu a Daura sakamakon cutar coronavirus ya yi mu'amulla da su kafin rasuwarsa.

Babban sakatare a ma'aikatar lafiya ta jihar, Dr Kabir Mustafa ya shaida wa BBC cewa tun bayan da suka samu labarin rasuwarsa suka nemi a debi samfur daga jikinsa domin yi masa gwaji.

Kuma bayan gano cewa cutar cornavirus ce ta kashe shi "sai muka garzaya wurin iyalinsa guda 13 inda muka dauki sunayensu da kuma samfurin majinarsu domin yin gwaji."

Dr Kabir ya kara da cewa sun kuma dauki mutum 20 wadanda ma'aikatan likitan da ya rasu ne " a jiya dai mun dauki mutum 33 sannan ma'aikatanmu sun duba rijistar mutanen da ke zuwa asibitinsa domin tabbatar da mutanen da ya yi mu'amilla da su tun bayan komawarsa jihar daga Ikko, kenan a yanzu haka muna jiran jin sakamakon dukkan wadannan mutanen.

A can kuma asibitin da ya rasu, tuni aka killace mutum hudu da suka yi mu'amilla da shi wannan mutum. Mun kuma shaida wa dukkanin wadanda suka yi mu'amilla da shi amma ba su da alamun cutar da su killace kansu."

Dama dai gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari ya ce likitan da ya mutu sakamakon kamuwa da coronavirus ya samo cutar ne daga Lagos.

Gwamna Masari ne ya tabbatar da BBC cewa cutar Covid 19 ce ta kashe likitan.

Ya bayyana cewa likitan mazaunin birnin Daura ne da ya yi bulaguro zuwa Lagos, kuma bayan dawowarsa ya kwanta jinya, wadda ta yi masa sanadi.

Gwamna Masari ya ce jami`ai sun dukufa wajen bin diddigin mutanen da likitan ya yi mu`amala da su domin gaggawar dakile bazuwar cutar a jihar.

Wannan ne karon farko da cutar ta bulla a jihar Katsina.