Covid-19: Mutum 6 sun sake kamuwa a Najeriya

Lokacin karatu: Minti 1

Hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa ta Najeriya NCDC, ta bayyana cewa an samu karin mutum shida da suka kamu da annobar coronavirus a kasar.

NCDC, ta wallafa hakan a shafinta na twitter da misalin karfe 9:30 na daren ranar Litinin 6 ga watan Afrilu cewa an sake samu karin mutanen da ke dauke da cutar.

Hukumar ta ce cikin wadanda suka kamu, 2 a Kwara suke, sai 2 a Edo da 1 a kuma Abuja babban birnin tarayyar kasar sannan 1 kuma a Rivers.

Ya zuwa yanzu dai akwai adadin mutane 238 da aka tabbatar sun kamu da cutar, inda 35 daga cikinsu sun warke, sai kuma 5 da suka rasu a Najeriyar.

A ranar 22 ga watan Maris ne hukumar ta bayar da sanarwar samun mutum na farko da ya mutu sakamakon wannan annoba a kasar.

Jihar Legas ce har yanzu take kan gaba a yawan masu dauke da cutar ta covid-19, kuma adadinsu ya haura 100 ya zuwa yanzu.

Jihohin da cutar ta bulla zuwa yanzu

Legas - 120

Abuja - 48

Osun - 20

Oyo - 9

Edo - 11

Bauchi - 6

Akwa Ibom - 5

Kaduna - 5

Ogun - 4

Enugu - 2

Ekiti - 2

Rivers -2

Benue - 1

Ondo - 1

Kwara- 2

Karin labaran da za ku so ku karanta