Covid-19: Kasuwar wayoyin zamani ta fadi warwas

A row of iPhone11 models on stands are arrayed in a neat line in this image

Kasuwar wayoyin zamani ta fadi warwas sakamakon illar da coronavirus ta yi ga tattalin arzikin duniya.

Wannan ne karo na farko da kasuwar wayoyin ta yi mummunan fadi tun bayan da aka fito da wayoyin zamani shekaru da dama da suka gabata.

Wani kamfanin bincike na Strategy Analytics ya bayyana cewa kasuwar wayoyin ta fadi da kusan kashi 38 cikin 100 a watan Fabrairu.

Barkewar coronavirus a China ta yi tasiri matuka kan wannan lamari, in ji Linda Sui wadda ita ce ta wallafa rahoton.

''Wasu kamfanoni da ke nahiyar Asia sun gaza kera wayoyin zamani, a wani bangaren kuma, 'yan kasuwa masu sarin wayoyi sun kasa zuwa kamfanonin domin sayan wayoyin,'' in ji ta.

Rahoton ya bayyana cewa kasuwar wayoyin zamani ta fadi daga miliyan 99.2 a Fabrairun 2020 zuwa miliyan 61.8 a Fabrairun 2020.

An kebe watan Fabrairu a matsayin wani lokaci babba ga kamfanonin wayoyi inda ake sa ran yin wani taron baje kolin wayoyi inda za a kaddamar da sabbin wayoyi a karon farko.

Taron na daga cikin manyan tarurrukan da aka soke sakamakon coronavirus.

Kamfanin Samsung wanda ya fitar da sabuwar wayar S20 a watan Fabrairu, ya bayyana cewa babu kasuwa sosai dangane da yadda ake sayar da wayar.

A wani bangaren, kamfanin Apple ya yi gargadin cewa da alama ba zai iya sanin riba ko faduwar da kamfanin zai samu ba kuma za a samu tarnaki matuka wajen sayar da kayayyakin kamfanin.

Binciken da aka gudanar ya shaida cewa kasuwar wayoyin zamanin za ta ci gaba da samun tarnaki cikin watan Maris sakamakon wannan annoba ta coronavirus ta bazu a Turai ta kuma kutsa har Amurka.

Miliyoyin kwastamomin wayoyi ne ke killace a gidaje a halin yanzu - wasu kuma ba su da niyyar fita domin sayan sabbin wayoyi.

Binciken ya ce masu shaguna za su iya bayar da garabasa domin su jawo masu sayen wayoyi.

Karin bayani kan coronavirus
Karin bayani kan coronavirus