Buhari ya ambaci Coronavirus a karon farko

Buhari

Asalin hoton, Presidency

Bayan fuskantar kakkausar suka daga 'yan Najeriya, daga karshe dai shugaba Buhari ya bara, inda ya yi gajeren tsokaci kan matakan da gwamnatinsa ke dauka dangane da cutar coronavirus.

Buhari a wani dan gajeren jawabi da ya yi wa tawagar ma'aikatan hukumar alhazai ta kasa ranar Juma'a, ya ce "muna aiki kafada da kafada da ma'aikatar lafiya domin ganin mun kare lafiyar 'yan kasarmu daga annobar Coronavirus."

Ya kara da cewa " a matsayinmu na gwamnati wannan ne abin da muka fi mayar da hankali a kai saboda haka ina kira a gare ku a tabbatar da cewa an samar da duk hanyoyin kariya daga kamuwa da cutar Coronavirus."

Wannan tsokaci na Shugaba Buhari na zuwa ne mako guda bayan da mai dakinsa ta wallafa a shafinta na Twitter cewa daya daga cikin 'ya'yanta na killace bayan komawa kasar daga Burtaniya.

'Yan Najeriya da dama dai sun yi ta sukar shugaban dangane da shirun da ya yi kan wannan cutar.

Da alama dai wannan bayanin nasa zai sa mutane da dama 'yan kasar da ba su amince da kasancewar cutar ta Coronavirus da farko ba, su yadda da ita su kuma dauki matakan kare kai.

Short presentational grey line

A baya dai mai magana da yawun shugaban, Malam Garba Shehu ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda ya ce 'yan kasar sun 'damu da batun Coronavirus'.

Garba Shehu a shafinsa na Twitter ya ce "yana mamakin yadda jama'a suka damu da cutar Coronavirus, bayan cutar zazzabin malaria ta fita kisa."

Wannan bayanin na Garba Shehu wanda ya ce ya yi shi ne domin radin kansa ya janyo suka daga 'yan kasar.

To sai dai a makon da ya gabata, fadar Shugaba Buhari ta bakin Garba Shehun ta yi wa 'yan Najeriya bayani kan dalilin da ya sa Buharin ya yi gum da bakinsa dangane da annobar Coronavirus.

Buhari

Asalin hoton, Presidency

Kakakin shugaban kasar Malam Garba Shehu, wanda ya shaida wa BBC hakan a wata hira ya ce yawan zuzuta batun zai tayar da hankalin 'yan Najeriya.

Shugabannin kasashe da dama suna yi wa 'yan kasarsu jawabi a kan halin da kasashensu ke ciki game da cutar.

Hasalima, Shugaba Muhammad Issoufou na Jamhuriyar Nijar, inda tun kafin a samu ko da mutum daya da ya kamu da cutar ba, ya yi wa 'yan kasar jawabi kan matakan da gwamnatinsa ke dauka domin yin riga-kafin cutar.

Da yammacin ranar Lahadi ne tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa dansa ya kamu da cutar Coronavirus kuma an kai shi asibitin koyarwa na Gwagwalada da ke Abuja.

Ya zuwa yanzu dai mutum 30 ne hukumar hana yaduwar cututtuka ta Najeriya, NCDC ta sanar.