Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Dan Atiku Abubakar 'ya kamu da coronavirus'
Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar ya ce dansa ya kamu da coronavirus.
Atiku Abubakar, ya bayyana hakan ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na twiiter.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce tuni aka kai dan nasa asibitin koyarwa da ke Gwagwalada a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya inda ake masa magani.
Atiku Abubakar ya bukaci al'umma da su saka dan na sa a addu'a.
Ya zuwa yanzu dai a hukumance akwai mutum 30 da suka kamu da cutar coronavirus a Najeriya, inda ake kyautata zaton cewa dan Atiku ne cikamakin mutum na 30 a jerin wadanda suka kamu da cutar a kasar.
Hukumar takaita yaduwar cutuka ta kasar dai ba ta sanar da suna ko wurin da wadanda suka kamu da cutar suke.
Mutanen da ke dauke da annobar coronavirus a nahiyar Afirka sun zarce mutum 1,000 a karshen wannan makon kamar yadda hukumar da ke yaki da cututtuka ta nahiyar ta bayyana.
Kasar Uganda ta bayyana mutum na farko da ya kamu da cutar a kasar inda kasar ta ce wani fasinja ne da ya zo daga Dubai.