China ta fusata da Trump kan kiran coronavirus ''yar China'

Asalin hoton, Getty Images
Kasar China ta fusata bayan shugaban Amurka Donald Trump ya kira cutar coronavirus "'yar China".
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar ta China ya gargadi Amurka a kan ta je ta ji da marsalolin da ke gabanta kafin ta tsangwami China.
An dai fara samun bullar coronavirus ne a birnin Wuhan na China a karshen shekarar 2019.
A makon da ya gabata ne mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Chinan ya yada wani batu inda ake zargin dakarun Amurka da kai cutar yankin.
Wannan zargi ne ya sa sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya bukaci China da ta daina yada abin da ba ta da tabbas a kansa.
Ya zuwa yanzu dai an samu mutum fiye da dubu dari da saba'in da suka kamu da cutar a fadin duniya inda mutum fiye da dubu tamanin suke a China.
A ranar Talata ne aka samu mutum guda da ya kamu da cutar a Beijing.
Me Donald Trump ya ce?
A ranar litinin 16 ga watan Maris din 2019 ne, Donald Trump ya wallafa wani sako a shafinsa na Twitter inda yake bayyana coronavirus a matsayin 'yar China.
Hukumar Lafiya Ta Duniya ta yi gargadi a kan danganta cutar da wani ko wata kungiya saboda gudun tsangwama.
Sakon Twitter da Mr Trump ya wallafa ya harzuka mahukuntan kasar China, inda mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Geng Shuang, ya ce wannan ba daidai ba ne domin zai iya janyo wa China tsangwama.
Mr Geng Shuang ya ce "Muna masu bukatar Amurka da ta gyara maganarta a kanmu, sannan ta daina mana kazafi".
Kamfanin dillancin labaran kasar ta China Xinhua ya ce kalaman Mr Trump alamu ne na wariyar launin fata da nuna kabilanci.


Ko ya dangantaka take tsakanin Amurka da China yanzu?
Dangantaka tsakaninsu a yanzu ta yi tsami.
Shugaba Trump ya jima yana zargin China da rashin kyautatawa a bangaren kasuwanci da cinikayya, yayin da ita kuma China ke ganin cewa Amurka na kokarin kawo mata cikas a bangaren ci gaban tattalin arzikinta.
Kasashen biyu sun samu babbar matsala a bangaren kasuwanci a tsakaninsu, abin da ya janyo dukkan kasashen suka sanya harajin a kan kayayyakinsu da ake shiga da su cikin kasashen biyu.











