Coronavirus: Amurka ta bukaci Iran ta saki 'yan kasarta da ke gidajen yari

Asalin hoton, AFP
Ga karin bayani daga sashenmu da ke lura da al'amuran da ke wakana a Iran, daya daga cikin wuraren da barkewar cutar ta fi muni baya ga kasar China.
Sakataren harkokin wajen Amurka ya yi kira ga Iran da ta yi la'akari da dalilai na jin kai ta hanzarta sakin daukacin Amurkawan da ke tsare a kasar, yayin da rahotanni ke cewa cutar Covid-19 ta yadu a cikin wasu gidajen yarin Iran masu cike da cunkoso.
"Amurka za ta dora laifi kai tsaye kan gwamnatin Iran idan wasu Amurkawa suka mutu. Kuma za mu hanzarta mayar da martani yadda ya kamata," Mike Pompeo ya yi wannan gargadi a wani furuci da ya yi a daren Talata.
Hukumomin bangaren shari'a na kasar Iran sun yi wa mutane 70,000 sakin wucin gadi daga cikin kimanin 189,500 da ake tsare da su a gidajen yarin kasar, a wani kokari na kula da barkewar cutar, wadda ta hallaka mutane a kalla 291, ta kuma kama wasu fiye da 8,000.
Sai dai mai rahoto na musamman na Majalisar Dinkin Duniya kan al'amuran kare hakkin bil'Adama a kasar Iran, Javaid Rehman, ya yi nuni cewa an saki wadanda ke zaman daurin kasa da shekara biyar ne kadai.
Mutanen da aka daure bisa dalilan na siyasa da wadanda aka daure fiye da tsawon shekara biyar game da shigar su cikin jerin zanga-zangar nuna kin jinin gwamnati, har yanzu suna nan tsare a jarun.
Mista Rehman ya shaida wa manema labarai a ranar Talata a Geneva cewa, ''Mutane da dan dama wadanda ke da nau'i dan kasa biyu, da 'yan kasashen waje suna cikin hadari na hakika...a gaskiya suna cikin wani yanayi mai ban tsoro''.
Ga karin labaran da za ku so ku karanta:











