Babu wanda zai iya shafe kasar Iran da al'adunta – Iran

Hassan Rouhani

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Tun farko Iran ta ce za ta dauki fansar kisan kwamandanta da Amurka ta yi
Lokacin karatu: Minti 3

Kasar Iran ta mayar wa da Donald Trump martani da cewa "dan ta'adda ne" bayan ya yi barazanar kai wa sansaninta 52 hari idan ta sake ta kai wa Amurka harin ramuwar kisan kwamandanta, Qassem Soleimani.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito kasashen Birtaniya da Oman da kuma Tarayyar Turai sun bukaci kasashen biyu da su kai zuciya nesa domin guje wa rikici.

Ministan Sadarwa da Yada Labarai na Iran, Mohammad Javad Azari-Jahromi, ne ya mayar da martanin a shafinsa na Twitter, inda ya kara da cewa "babu wanda zai iya rushe kasar Iran da al'adunta".

"Kamar ISIS da Hitler da Genghis! Dukkansu ba sa kaunar al'adu. Trump dan ta'adda ne da rigar shugabanci. Nan gaba kadan zai koyi darasi cewa babu wanda ya isa ya karya kasar Iran da al'adunta," in ji Mohammad Javad.

Kauce wa X, 1
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 1

Barazanar Trump

Donald Trump

Asalin hoton, Getty Images

Tun farko Shugaba Donald Trump ya ce kasarsa ta shirya kai hare-hare a wasu wurare 52 masu muhimmanci ga Iran idan ta taba kasarsa.

A sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Trump ya ce muddin Iran ta taba Amurkawa ko kadarorin Amurka, to Amurka ba za ta yi wata-wata ba wajen mayar da martani.

Ya ce a shirye kasarsa take ta sanya kafar wando daya da Iran din da ta dade tana addabar jama'a.

Sakon nasa na zuwa ne yayin da kasashen biyu ke ci gaba ta tayar da jijiyoyin wuya bayan Amurka ta kashe babban kwamandan sojin Iran a Iraki Qasem Soleimani, a wani harin sama a Iraki.

A baya dai Trump ya ce gwamnatinsa ta kashe Soleimani wanda ya zarga da kitsa hare-haren da Iran ke kai wa kasarsa ne domin guje wa yaki. Amma a sakon nasa na tuwita ya ce Soleimani ya yi sanadiyyar mutuwar daruruwan mutane kuma yana da hannu a harin da aka kai wa ofishin Amurka a Iraki da ma wasu wuraren.

Kauce wa X, 2
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 2

A nata bangaren Iran ta lashi takobin yin mummunar ramuwar gayya game da kashe janar din nata wanda za a yi jana'izarsa ranar Talata 7 ga watan Janairun da muke ciki.

Da yake mayar da martani game da barazanar da Iran ta yi na kai wa kadarorin Amurka a ta shafinsa, shugaban Amurkan ya ce kasarsa ta riga ta ayyana wasu wurare 52 masu muhimmanci ga Iran da Amurkan za ta kai hari idan har Iran ta taba Amurka.

Kauce wa X, 3
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 3

Ya ce kasarsa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen kai zafafan hare-haren da Iran ba ta taba ganin irinsu ba. Adadin wuraren a cewarsa, ya yi dai-dai da na Amurkawan da Iran ta yi garkuwa da su a shekarun baya.