Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ba zan kalubalanci cire ni daga sarauta ba – Sarki Sanusi
Tsohon sarkin Kano Muhammadu Sanusi na II ya ce ya riga ya yi gaba ba zai kalubalanci cire shi da gwamnatin Kano ta yi daga sarauta ba.
Sanusi wanda aka dauke shi a wani gajeren bidiyo yana magana da wasu mutane cikin harshen Turanci bayan isarsa Lagos, ya ce da zai je kotu da ya samu nasara saboda wasikar da gwamnatin ta rubuta cike ta ke da kura-kurai.
"Kwata-kwata hujjojin da aka bayar a wasikar ba a rubuta su da kyau ba, abu ne mai sauki in tafi kotu in samu nasara idan ka duba abin da ke cikin wasikar," in ji shi.
"Kotu za ta yi tambayoyi kamar haka; Shin kun tuntube shi? Kun nemi jin ta bakinsa? Kun ba shi dama ya kare kansa? Idan amsoshin a'a ne, shi ke nan za a sami nasara.
"Amma ba zan je kotu ba, gara in fuskanci rayuwa ta gaba kuma."
Ina Muhammadu Sansusi II yake yanzu?
Da yammacin ranar Juma'a ne tsohon Sarki Sanusi ya bar kauyen Awe na Jihar Nasarawa tare da rakiyar gwamnan Kaduna Malam Nasir El-Rufai.
El-Rufai wanda abokin tsohon sarkin ne, ya raka shi har kofar jirgin da ya shiga zuwa Legas a Abuja.
Tun farko dai kauyen Loko aka kai shi a Jihar ta Nasarawa, inda ya wayi garin Talata a can.
A ranar Juma'a kuma wata Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta bayar da umarnin bai wa tsohon Sarkin na Kano damar shiga ko ina a Najeriya ban da Jihar Kano.
Lauyoyin tsohon sarkin ne suka shigar da kara suna kalubalantar abin da suka kira tauye masa hakkin walwala da kundin tsarin mulki ya ba shi bayan da aka tsare shi a kauyen Loko kafin a mayar da shi garin Awe a Jihar Nasarawa daga baya.
Hotunan da gwamnatin Jihar Kaduna ta wallafa a shafinta na Twitter ranar Juma'a sun nuna yadda gwamna El-Rufai ya raka tsohon sarki Sanusi har kofar jirgin da ya hau zuwa Legas.