Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mece ce manufar El-Rufa'i ta bai wa Sanusi II mukamai?
Tun bayan da gwamnan jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya Mallam Nasir El Rufa'i ya sanar da bai wa tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II mukamai, mutane suke ta dasa ayar tambaya kan dalilan da suka sa gwamnan ya dauki matakin.
Ranar Litinin gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya cire sarkin daga gadon sarauta saboda "rashin biyayya da gwamnatinsa" da tsohon sarkin ya yi tare da maye gurbinsa da Aminu Ado Bayero wanda aka yi bikin mika masa takardar aiki da sandar girma ranar Laraba.
Wani mai sharhi kan al'amura kuma malami a Jami'ar Jihar Kaduna, Dr Tukur Abdulkadir, ya bayyana wa BBC dalilan da suka sanya Gwamna El Rufa'i ya bai wa Sarki Sanusi II mukamai biyu a kwana kadan bayan an cire shi daga gadon sarauta.
Siyasa
Dr Tukur Abdulkadir ya ce za a iya cewa akwai manufa ta siyasa a mukaman da Gwamna El Rufa'i ya bai wa Sarki Sanusi II.
"Ana rade-radin shi gwamnan jihar Kaduna yana cikin wadanda za su iya fitowa su kara taka rawa a harkar siyasa ta kasa ba ta jiha ba," in ji Dr Abdulkadir.
Ya kara da cewa wasu na ganin hakan wata dabara ce ta kara wa kansa kima sai dai "wasu na tunanin manufarsa ita ce kara fito da tasiri da mutuntaka da yake ganin shi 'tubabben sarki' yana da su."
A ganinsa, hakan na iya kara wa tsohon sarkin fitowa fili tun da da ma sananne ne kuma kila wani al'amari ne da zai kara masa tasiri da wasu manufofi da ba lallai ne a fahimci manufofin a yanzu ba.
Alaka mai karfi
Malamin ya kuma ce ta wata fuskar, matakin bai wa tsohon sarkin mukamai na da alaka da kyakkyawar dangantakar da ke tsakanin gwamnan jihar Kaduna da tsohon Sarkin Kano.
A cewarsa, "Wannan al'amari ba abin mamaki ba ne saboda irin alakarsu da dangantakarsu."
"Duk mutumin da kuke da kusanci ko ta siyasa ko ta zamantakewa, a lokacin da kake cikin yanayi na jarrabawa ko halin ni-'ya-su, a wannan lokacin aka fi samun wanda zai tuna da kai.
"Watakila shi [El Rufa'i] ya yi ne domin ya nuna cewa abokantakar tasu ta gari ce kuma ya nuna cewa yana tare da shi a cikin kowanne hali yake ciki," kamar yadda mai sharhin ya fada.
Tasirin mukaman kan Sarki Sanusi II
Sai dai kuma masanin ya ce akwai tasirin da wannan mataki na gwamnatin Kaduna zai yi a kan Sarki Sanusi II, "babban tasirin shi ne zai kara tabbatar da cewa ba zai kasance kamar wasu daga cikin sarakunan baya ba, wadanda idan irin wannan hali ya fada musu sukan kasance kamar ma ba sa duniya.
Amma sanin da aka yi wa shi tsohon sarkin tun da ba mutum ne mai shiru kan al'amuran yau da kullum ko harkar tsaro ko tattalin arziki da shugabanci ba, wadannan mukamai za su kara masa tasiri da ci gaba da taka rawar da aka san yana takawa," in ji Dr Abdulkadir.
Malamin ya kuma ce "zai kara hada wasu manufofi da ba lallai ba ne su bayyana a yanzu, abu ne da zai kasance tagomashi gare shi da wadannan hukumomi musamman wadanda aka ba shi damar ba da gudummawa a cikinsu."