Kashi 60% na 'yan firamare ba sa iya biyan kudin makaranta a Zimbabwe

Asalin hoton, Anadolu Agency
Dubban yara ne suke barin makarantun firamare a Zimbabwe yayin da tattalin arzikin kasar ke kara tabarbarewa ta yadda iyaye ba sa iya biyan kudin makaranta da kuma fari da ake fama da shi.
A shekarar da ta gabata, kashi 60 cikin 100 na yaran firamare aka kora daga makarantu saboda ba su biya kudin makaranta ba.
Shekarar karatu ta fara ne tun a watan Janairu, amma a kwalejin Fanta da ke unguwar Epworth ta marasa galihu a Harare babban birnin kasar, har yanzu wasu azuzuwa a kulle suke.
Mai makarantar, Perkins Chimhete ya bayyana cewa an samu raguwa sosai ta shigar sababbin dalibai.
"Ga su nan zube amma iyayensu ba su da kudi, kuma ba wai wata makarantar suka shiga ba," in ji Chimhete.
Tun a shekarun 1990 ne aka daina bayar da ilimi kyauta a kasar ta gabashin Afirka.
Iyaye kan biya kudi daga dala 30 (kusan N11,000) zuwa 700 (kusan N255,000) a shekara a matsayin kudin makaranta.
Iyaye na ta saka yaransu a makarantu masu araha wadanda ba su da rajista da hukuma, inda suke biyan dala uku kacal a wata - kwatankwacin naira 1,000.
Hakan na nuna kaguwar da mutane suka yi, ganin yadda makarantu na wucin gadi ke kara yawa musamman a Epworth.
Ana kafa makarantu a gidajen mutane da kuma kwararo.
Wata shugabar makaranta mai suna Eunice Maronga ta ce: "Wasu na iya biya, wasu kuma ba sa iyawa. Wasu kan biya dalar Zimbabwe 20, sati na gaba su biya 15 har sai sun biya duka."
Sai dai makarantar N1,000 a wata tana da nata irin yanayin - babu abin zama sannan malamin ne kadai mai littafin karatu.
Amma duk da haka yawan yaran da ake sakawa a wadannan makarantun ya ragu da kashi uku idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata.
Alkaluman Majalisar Dinkin Duniya sun nuna cewa yara sama da 20,000 ne suka daina zuwa firamare a 2018, kashi 20 cikin 100 kuma suka daina zuwa karamar sakandare.










