Burundi: An gano manyan kaburbura fiye da 4,000

Asalin hoton, CVR
An gano manyan kaburbura fiye da 4,000 a Burundi, sakamakon wani bincike da Hukumar Binciko Gaskiya da Sasantawa kan rikicin da kasar ta fada tun da ta samu 'yancin kai a 1962.
Hukumar, wacce aka kafa a 2018 don ta yi karin haske kan rashin jituwar da ake fuskanta, ta ce ta gano mutum 142,505 da aka kashe.
An yi kisan kiyashin ne a shekarun 1965 da 1972 da 1988 da kuma 1993.
Ana zargin 'yan siyasar Burundi da gwara kan 'yan kabilar Tutsi marasa rinjaye da kuma 'yan kabilar Hutu masu rinjaye.
Shugaban hukumar Pierre-Claver Ndayicariye ne ya gabatar da rahoton ga majalisar dokokin kasar.
"Akwai manyan kaburbura da dama da har yanzu ba a kai ga gano su ba, saboda mutanen da suka san su ko dai suna tsoron magana ko kuma suna cikin halin kaduwa har yanzu," a cewarsa.
Ya kara da cewa gano ainihin abin da ya faru zai iya kai wa ga yafiya tsakanin wadanda suka kitsa rikicin da kuma iyalan wadanda aka kashe, don samar da dauwammmen zaman lafiya a Burundi.
A ranar Litinin an bude wani kabari da aka binne mutum 270 inda mutane daga babban birnin kasar Bujumbura.
An yi amanna cewa kabarin na kunshe da gawarwakin mutanen da aka kashe ne bayan kisan gillar da aka yi wa Melchior Ndadaye, shugaban kasar dan kabilar Hutu na farko a 1993.
Kisan ya haifar da mummunan yakin basasa tsakanin 'yan kabilar Tutsi da suka mamaye rundunar sojin kasar da kuma kungiyoyin 'yan tawaye na 'yan kabilar Hutu.
Fiye da mutum 300,000 ne suka mutu a yakin da aka shafe shekara 12 ana yi.
Wasu mutanen da suka ziyarci kabarin a Bujumbura sun iya gane mutanen da suka sani daga tufafinsu da kuma katinansu na shaida.
"Mutane sun yi ta kuka kuma hankula sun tashi," a cewar mataimakin shugaban hukumar yayin hirarsa da BBC.












