Abu 9 game da sabuwar bizar Najeriya

Shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba hannu akan sabon tsarin bizar Najeriya na 2020

Asalin hoton, @BashirAhmaad

Bayanan hoto, An fara gabatar da tsarin bizar Najeriya na farko a 1958, wato zamanin mulkin mallaka

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gabatar da tsarin bizar kasar na shekarar 2020 ga 'yan kasa a ranar Talata. Sai dai abin tambayar shi ne, me hakan ke nufi?

Mai magana da yawun shugaban Femi Adesina ya amsa wannan tambaya, inda ya bayyana abu 9 game da sabuwar bizar kamar haka:

  • An shafe lokaci mai yawa na shekarar 2019 wurin tsara sabuwar bizar ta hanyar yin taruka, kara wa juna sani, horarwa, ganawar masu ruwa da tsaki na hukumar shige da fice ta Immigration a biranen Legas da Benin da Abuja, a watan Agusta da Oktoba da Disamba.
  • Tana da tsari kamar na sauran kasashen duniya kamar dangwalen yatsa, wanda ke manne da bayanan kowane mutum
  • Bizar tana da aji uku: mai gajeren zango, ta wucin gadi, da kuma ta zaman dindindin
  • Yanzu rukuni 79 ake da su sabanin ta baya, inda ake da shida kacal
  • Akwai biza ga wadanda aka haifa a Najeriya amma suke zaune a kasashen waje, masu fasfon kasa biyu
  • Bizar nan-take (bayan an isa Najeriya) amma ta gajeren zango
  • Ta intanet za a rika biyan kudi babu maganar hannu da hannu
  • Sabuwar bizar wani bangare ne na sabon tsarin hukumar shige da fice na 2019-2020
  • Tana da alfano ga tattalin arzikin Najeriya
Shugaba Muhammadu Buhari tare da shugabannin hukumar kula da shige da fice

Asalin hoton, @NGRPresident

Wani babban abu da ke da muhimmanci a tsarin shi ne, binciken fasahar zamani ga matafiya da gwamnatin ta ce tana sa rai zai taimaka wajen tabbatar da tsaro da kuma aniyar gudanar da lamura a bude da kuma kare yaduwar cin hanci da rashawa.