Ribar tarukan kasuwanci da zuba jari da Buhari ke halarta

@

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Sagiru Kano Saleh
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Broadcast Journalist

Shugaban Najeriya na halartar taron koli kan zuba jari da Birtaniya ta shirya tsakaninta da kasashen Afirka da nufin kulla sabbin huldodin kasuwanci domin kara bunkasa tattalin arzikinta.

Taron wanda shi ne irinsa na farko da Birtaniya, mai neman ficewa daga Tarayyar Turai a karshen watan Janairun da muke ciki ta shirya, ya gayyato gwamnatoci da 'yan kasuwa da ma cibiyoyin kasa da kasa domin su tallata irin albarkatun da Afrika ke da su.

Sannan su tallata damar da 'yan kasuwa ke da ita na bunkasa harkokinsu ta hanyar zuba jari da samun riba a nahiyar.

Firai Minista Boris Johnson zai yi amfani da damar wajen tallata kasarsa a matsayin wadda ta fi dacewa kasashen Afirka su runguma wajen yin huldar cinikayya, musamman bayan ficewar kasarsa daga Tarayyar Turai.

Ana ganin taron a matsayin daya daga cikin matakan da Birtaniya ke dauka masu alaka da ficewarta daga Tarayyar, wanda zai haifar da sauye-sauye a huldodinta na cinikayya da kasashe.

Taron na Birtaniya ya mayar da hankali ne kan batun cinikayya tsakanin bangarorin da bunkasa tattalin arzikinsu da tallafa wa ci gabansu da kuma samar da makamashi maras gurbata muhalli.

A baya ma an gayyaci shugaban Najeriya Muhammadu Buhari wanda ke cikin shugabannin Afirka 15 da suka samu halartar taron, zuwa ire-iren wannnan taro a wasu manyan kasashe.

A lokacin tarukan na baya Buhari da gwamnatoci da kuma kamfanonin kasashen sun kulla yarjejeniyoyi da nufin jawo karin masu zuba jari zuwa Najeriya da kuma kawo wa kasarsa ci gaba.

Bayan haka kasar ta kuma dauki wasu karin matakai da suka hada da fito da wasu tsare-tsare a kan hajoji da kamfanoni na 'yan kasashen waje da nufin ba su kwarin gwiwar yin kasuwanci a Najeriya.

Kusan dukkan manyan kasashen duniya sun mika wa Najeriya irin wannan gayyata, kama daga China da Rasha da Jamus da Amurka da kuma Birtaniya a yanzu.

Shin wace riba kasar ta samu daga yarjejeniyoyin da ta sanya hannu a kai?

Wannan layi ne

Muhimmancin tafiye-tafiyen Buhari

Masu sharhi da masana tattalin arziki na cewa halartar irin wadannan taruka na da muhimmanci ga Najeriya.

Gayyatar da shugaban ke samu zuwa tarukan na nuna yadda manyan kasashe ke ganin kimar Najeriya da Shugaba Buhari tare da tunanin za su amfana ta hanyar huldar kasuwanci da Najeriya.

Ta fannin diflomasiya kuma, shugabanni masu kima ne manyan kasashe kan gayyata domin su tattauna. Bayan haka halartar tarukan da shugaban kasar ke yi zai taimaka wajen tallata kasar a idon duniya.

Wannan layi ne

Ribar da Najeriya ta samu

'Yan kasar sun sha bamban game yadda suke ganin tasiri ko ribar da kasar ta samu daga irin wannan ziyarar da ake gayyatar shugaban kasar.

Daga cikinsu akwai masu korafi cewa har yanzu ba a aiwatar da akasarin yarjejeniyoyin da shugaban ya kulla da kasashen ba a lokacin irin wadannan ziyara.

Daga cikin akwai wadanda suka kosa cewa har yanzu ba a fara aiwatar da yarjejeniyar samar da wutar lantarki da kasar ta kulla da Jamus yadda ya kamata ba.

A fahimtarsu, yarjejeniyar wutar lantarkin na cikin wadanda kasar za ta fi amfana da su idan aka aiwatar da ita kamar yadda aka kulla.

Suna kuma nuni da cewa ba a aiwatar da yarjejeniyar da Najeriyar ta kulla da China kan amfani da kudaden kasar China maimakon dalar Amurka a wajen huldar cinikayya ba.

Kazalika 'yan China ba su zo sun kafa kamfanoni a kasar kamar yadda aka yi alkawari ba.

Amma kuma wasu 'yan kasar na ganin cewa yarjejeniyar samar da takin zamani da kasar ta kulla da Moroko ta biya bukata, domin a cewarsu sun gani a kasa, inji Farfesa Garba Ibrahim Sheka, masanin tattalin arziki.

Farfesa Sheka ya bayyana cewa akwai alamun batun aiwatar da yarjejeniyar wutar lantarkin za ta taso nan ba da jimawa ba idan aka yi la'akari da yadda gwamantin kasar ke magana kan batun a baya-bayan nan.

A cewarsa, yawancin manyan kasashen da ke neman kulla alakar cinikayya da kasashen Afirka na yin haka ne domin samun ciniki idan aka yi la'akari da yawan mutanen nahiyar.

Wannan layi ne

"Bayan haka 'yan kasuwar kasar da ke halartar irin wadannan taruka kan samu riba ta yadda suke samun damar kulla huldar kasuwanci a kasashen.

"Kasashen da ke gayyatar Najeriya na da manufofinsu da kuma bukatun da suke nema cimmawa daga kasashe masu tasowa irin Najeriya.

"A don haka sun fi mayar da hankali wurin cika alkawuran da suka ga bukatunsu za su biya.

"A wani lokaci kuma yarjejeniyoyin na tattare da wasu sharudda ko ka'idodi masu wuyar cikawa, wanda sakamakon haka ba a iya aiwatar da su yadda aka tsara," in ji shi.

Farfesa Sheka ya ce yawanci in ban da China wadda kan bayar da kudaden da ta yi alkawari da sauransu, abin da sauran kasashen ke ba wa kasashe masu tasowa bai wuce lamuni ko bashi ba.

Ya ce "duk da haka kasashen ba su fiye zuwa Afirka domin bude kamfanoni da masana'atu domin samar da ayyuka yadda kasashen nahiyar ke bukata ba."

Wannan layi ne

Ina matsalar take?

Gaskiyar magana ita ce duk kasashen da ke neman kulla alaka da Najeriya ko sauran kasashen Afirka, makasudinsu shi ne samun riba ta kai tsaye ko a kaikaice.

Don haka su kasashen masu neman a kulla irin wannan alaka kan ayyana bukatun da suke neman cimmawa gwargwadon manufofin kasashensu da kuma matakan aiwatar da su tun kafin su kira taro.

Su ke da cikakkiyar sani da shiri game da abun da taron ya kunsa da yadda za su bijiro da abin da suke bukata ga mahalarta.

Akasari masu masaukin baki ne ke tsara yarjejeniyoyin da sharudda da kuma ka'idojinsu sannan su gabatar wa baki a lokacin tattaunawa domin rattaba hannu.

Ana iya cewa mahalarta taron ba su da wadataccen lokacin yin nazari mai zurfi da ma tuntubar juna ta a cikin kurarren lokacin.

Duk da cewa a wasu lokutan kasashe masu tasowa kan gabatar da nasu bukatun, masana na ganin bukatunsu ya fi karkata ne a neman tallafi.

Bayan haka manyan kasashe ke da wuka da nama domin sun fi bayar da kaso mai yawa na kudaden na hadin gwiwa da ake bayarwa domin ci gaba a kasashe irin Najeriya.

Shi ya sa yawancin ake ganin tamkar kasashe masu tasowan kan halarci irin wadannan tattaunawa ne dauke da kokon bara, inji Farfesa Sheka.

A wasu lokuta kuma kasashe irin Najeriya ba su cika nasu bangaren alkawarin da zai ba wa turawa kwarin gwiwan cika nasu bangaren.

Akwai kuma yiwuwar Manyan kasashen su ki mayar da hankali a kan duk huldar da suka ga ba za su samu ribar da suka yi tsammani ba a kai.

Bugu da kari kasashe irin Najeriya ba su da karfi ta fuskar masana'antu da sarrafa albarkatun kasashensu ta yadda za su iya kwadaita wa manyan kasashe su shigo cikin natsuwa.

Kazalika ci gaba ta fuskar fasahar zamani wanda shi ne babban abin da duniya ke bukata a yanzu na da karanci a kasashen Afirka idan aka kwatanta su da takwarorinsu.

Ya ce saboda haka akwai yiwuwar manyan kasashe su ne za su fi cin moriyar irin wannan alaka duba da yadda kasuwancin zamani ke tafiya.

Za su ci gaba da shigo da kayakin da suka sarrafa a kasashensu, ko da kuwa daga Najeriya aka samu kayan da ake bukata domin hakan.

Wannan layi ne

Kasuwar hannun jari

Rahoton da kasuwar hada-hadar hannun jarin Najeriya ta fitar a baya-bayan nan ya ce 'yan kasashen waje sun janye hannun jarin naira biliyan 491 daga kasuwar a tsakanin Janairu zuwa Nuwamban shekarar 2019.

Rahoton ya ce adadin hannayen jarin da 'yan kasashen wajen suka janye ya haura kashi 20.4% na adadin da suka janye a bara.

Farfesa Sheka ya ce hakan na da ban mamaki ganin cewa babu wata babbar barazanar tsaro a fili a kasar.

"Baya ga zuba jari domin samun riba kai tsaye, 'yan kasuwa kan zuba jari domin cin riba daga darajar kudin kasashen da suka zuba jari.

"Neman daidaita farashin naira da Najeriya ke yi na iya kasancewa dalilin da ya jawo janyewar 'yan kasuwar.

"Irin wadannan 'yan kasuwa kan sayi hannun jari a kasashen da darajar kudinsu ta fadi, ta yadda cikin dan lokaci kudin za su samu riba mai yawa.

"Yanayin tattalin arzikin kasashensu na iya zama dalilin mayar da kudadensu gida.

"A yayin da mutane ke fitar da dukiyoyinsu daga kasashensu zuwa wasu kasashe domin samun riba, rashin samun riba fiye da na kasashensu na iya sa su mayar da kudadensu gida.

"Bayan haka tafiyar hawainiya da tattalin arzikin wasu kasashen Turai ke fama da shi kan sa wasu 'yan kasashen waje mayar da kudadensu gida domin kishin kasa da zummar taimaka wa wajen farfado wa da tattalin arzikin kasashensu," in ji Farfesa Sheka masanin tattalin arzikin.

Wannan layi ne

Mene ne abin yi?

Ga jerin matakan da masana tattalin arziki suka ce ya kamata kasar ta yi:

  • Sun nuna bukatar kasar ta bibiyi yarjeniyoyin da ta kulla a irin wadannan taruka ko gayyata da aka yi mata domin tabbatar da aiwatar da su yadda ya kamata.
  • Sannan wajibi ne kasar ta tabbata tana cika nata bangaren alkawarin ko ka'idoji da sharuddan da yarjeniyoyion suka kunsa.
  • Ya kamata kasar ta inganta albarkatunta yadda ya kamata ta yadda za ta iya tallata su ga kasashen a yayin kulla wasu yarjejeniyoyin.
  • Akwai kuma bukatar kasar ta rika yi wa alkawuran nazari mai zurfi domin fahimtar irin abin da abin da suka kunsa da irin tasirin da za su yi da ma yiwuwar aiwatar da su.
  • Tun kafin halartar irin wadannan zama akwai bukatar Najeriya ta samu kyakkyawar fahimtar abin da taron ya kunsa da abin da za a bukata daga gareta sannan ta dauki matsayi tun kafin lokacin.
  • Kafin ta rattabata hannu, yana da muhimmanci kasar ta tabbatar cewa shirye take kuma za ta samu moriya ta zahiri a yarjeniyoyin yadda ya kamata.
  • Kasar ta kasance ita ma tana gindaya sharudda tare da mika bukatun da suka dace da yanayinta ba wai sai abin da aka yi mata tayi ba.
  • Yana da kyau kasar ta guji yin gaggawa sannan ta yi kyakkaywan shiri da fahimta kafin ta shiga irin wadannan yarjejeniyoyi.