Kashi casa'in na mutanen da Boko Haram ta kashe Musulmai ne — Buhari

Buhari

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Buhari yana yin ta'aziyya ne kan kisan Rabaran Lawan Andimi da aka kashe a jihar Adamawa a watan Janairu

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya shaida wa kafafen watsa labarai cewa akasarin mutanen da mayakan Boko Haram suka kashe Musulmai ne, yana mai cewa burin 'yan kungiyar shi ne su yi amfani da addini wajen raba kan 'yan kasar.

A wata makala da ya rubuta wadda aka wallafa a Jaridar Christianity Today, Shugaba Buhari ya ce bai kamata a kyale mayakan Boko Haram su raba kan 'yan Najeriya ba.

"A hakikanin gaskiya, kashi 90 cikin 100 na mutanen da rikicin Boko Haram ya shafa Musulmai ne: cikinsu har da 'yan makaranta mata Musulmai 100 wadanda aka sace tare da takwararsu Kirista guda daya, da kai hare-hare a masallatai da kuma kashe fitattun Malaman addinin Musulunci."

"Wadannan 'yan ta'adda suna so su gina katanga da za ta raba tsakaninmu. Sun gaza a yunkurinsu na hare-haren ta'addanci, don haka yanzu suna so su raba kanmu ta hanyar sanya mu sukar juna."

Shugaban kasar ya rubuta makalar ne domin yin jaje da alhinin kisan da wasu da ake zargi mayakan Boko Haram ne suka yi wa wani limamin Kirista, Rabaran Lawan Andimi bayan da suka sace shi.

An halaka Lawan Andimi ne a karamar hukumar Michika ta jihar Adamawa bayan an yi garkuwa da shi a farkon watan Janairun wannan shekara a wani hari da 'yan Boko Haram suka kai a kauyensu.

Kwanaki kadan bayan da aka yi garkuwa da shi an ga marigayin, a wani bidiyo da 'yan kungiyar Boko Haram din suka saki, yana rokon gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Fintiri ya ceci rayuwarsa.

Wani rahoto da cibiyar Tony Blair Foundation ta fitar a watan Janairun 2020 ya ce kungiyoyin da ke da'awar jihadi sun fi kashe Musulmi fiye da mabiya wani addini a duniya.

Rahoton cibiyar da ta ce ta yi bincike da sa ido kan ayyukan ta'ddanci tun a 2017 a duniya, ya ce kashi 70% na wadanda aka kashe Musulmi ne wadanda ba su ji ba su gani ba.

Kazalika, wani rahoto na asusun yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya ce fiye da malaman makaranta 2,295 Boko Haram ta kashe a 2017 a jihar Borno.

Ya kara da cewa an raba 19,000 da muhallansu, sannan kuma makarantu 1,400 suka lalace a shekara takwas din da aka shafe ana rikici a yankin.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce akalla mutum 27,000 ne suka rasa rayukansu a tsawon shekara 10 na rikicin Boko Haram a jihohin Adamawa da Borno da kuma Yobe.

A watan Yulin 2019 ne aka cika shekara 10 da kashe Shugaban kungiyar Boko Haram na farko Muhammad Yusuf.