Boko Haram ta kashe malamai 2,295 a Borno - UNICEF

Wadansu da dama na samun iliminsu ne a matakin farko a sansanonin 'yan gudun hijira.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Yara da dama na samun iliminsu ne a matakin farko a sansanonin 'yan gudun hijira.
An wallafa

Asusun Kula da Yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF, ya ce har yanzu mafi yawan makarantun jihar Borno inda rikicin Boko Haram ya fi kamari a rufe suke, wanda aka danganta hakan da cewa 'yan kungiyar na kai hare-haren ne da gayya don lalata fannin ilimi.

A wani rahoto da ta fitar a ranar Juma'a, UNICEF ta ce a kalla kashi 57 cikin 100 na makarantun Borno a rufe suke, a yayin da aka fara sabuwar shekarar karati, inda yawan malaman ya ragu kuma gine-ginen makarantun suke a lalace.

A wata sanarwa da UNICEF ya aikawa manema labarai ya ce, fiye da malamai 2,295 aka kashe, yayin da aka raba 19,000 da muhallansu, sannan kuma makarantu 1,400 suka lalace a shekaru takwas din da aka shafe ana rikici a yankin.

Makarantun sun kasance a rufe ne saboda yadda aka lalata su, wasu kuma suna yankunan da har yanzu babu tabbataccen tsaro, duk kuwa da irin yadda sojoji ke kokarin 'murkushe' 'yan kungiyar tun a shekarar 2015.

UNICEF ya yi gargadi cewa lamarin na barazanar sanyawa a rasa yara masu tasowa, inda hakan zai rushe duk wani buri na makomarsu da makomar kasarsu idan har ba a yi komai ba kan hakan.

Mataimakin hukumar ta UNICEF Justin Forsyth, ya kai ziyara yankin arewa maso gabashin Najeriyar, inda ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa: "koma bayan da hakar ilimi ta fuskanta sakamakon ta-da kayar baya ba tsautsayi ba ne."

"Wannann wani abu ne da Boko Haram ta shirya yin sa da gayya, don hana yara samun ilimi," a hirar tasa da AFP.

Mista Forsyth ya kara da cewa, kusan yara miliyan uku na bukatar taimakon gaggawa ta fannin ilimi, sai dai akwai wawagegen gibi a kudaden da UNICEF ke samar wa don yin ayyuka a yankin.

Kusan yara 750,000 ne suka samu komawa makaranta a bana a jihohin Borno da Yobe da Adamawa, jihohin da su ma ayyukan Boko Haram suka yi wa illa.

Wadansu da dama na samun iliminsu ne a matakin farko a sansanonin 'yan gudun hijira.