Abin da ya kai Turai ‘Yaradua Aso Rock

A

Asalin hoton, Aisha Buhari/Instagram

Mai dakin shugaban Najeriya, Aisha Buhari da matar tsohon shugaban kasar, Turai Yar'adu sun gana a fadar shugaban kasar.

A wani sako da ta wallafa a shafinta na Instagram ranar Talata, Aisha Buhari, ta ce sun tattauna kan batutuwa da dama ciki har da cin zarafin mata da shan miyagun kwayoyi.

"Na ji dadin ganin Mrs. Yar'adua cikin koshin lafiya, kuma mun tattauna kan batutuwa da dama da suka hada da cin zarafin mata da shan miyagun kwayoyi da ci gaban matasa a Najeriya," in ji ta.

Ta kara da cewa ta saurari ra'ayin matar tsohon shugaban kasar kan wadannan batutuwa, inda kuma ta kewaya da ita bangarorin fadar shugaban kasar, lamarin da ya tuna mata lokacin da take fadar.

Ta kuma duba hotunan matan tsofaffin shugabannin Najeriya da aka dasa a dakin taron, abin da ta bijiro da shi a lokacinta domin karrama dukkanin matan tsofaffin shugabannin kasar.

Turai Yar'adua ita ce mai dakin marigayi tsohon Shugaban Najeriya na 13 Umaru Musa Yar'adua wanda ya mulki kasar daga 2007 zuwa 2010.

Ta kasance mai karfin fada a-ji a mulkin mijinta saboda yadda ta kasance daya daga cikin mashawarta ga 'Yaradua a lokacin da yake mulki.

Wasu rahotanni sun nuna yadda Turai ta rika yin tasiri wajen zaben wasu daga cikin jami'an gwamnati da za su ba da gudummawa a gwamnatin mijinta.

A

Asalin hoton, Aisha Buhari/Instagram

Ta kuma kasance gaba-gaba a jinyar mijinta marigayi Shugaba Umaru Musa 'Yar adua wanda ya yi doguwar jinya a kasar waje.

Har ma wasu rahotanni na cewa sai wanda ta so yake ganinsa cikin manyan mukarrabansa da ke zuwa duba shi.

Sabanin Aisha Buhari wadda a lokacin da Buhari yake duba lafiyarsa a kasar waje, ba su tafi tare ba.

Turai da Aisha Buhari dai na da kamanceceniya ta bangarori da dama musamman ta wajen gayu da sanya sutura ta yayi, kamar yadda matan Najeriya suka shaida.

Sai dai sun sha bamban ta wasu wuraren kamar karfin fada a ji a gwamnatin mazajensu, yayin da ake ganin Turai ta samu wannan damar, ita Aisha ana ganin kamar ta rasa irin ta musamman ganin yadda ta sha furta hakan.

Sannan ana yi wa Aisha Buhari kallon mai yawan jano ce-ce ku-ce.

Misali, Aisha Buhari ta fito karara ta soki gwamnatin Buhari saboda a cewarta, akwai abubuwa da dama da ba sa tafiya yadda ya kamata.

Wannan dai ya zo wa da 'yan Najeriya da ba-zata ganin yadda Aisha ta caccaki gwamnatin mijinta a wata babbar kafar yada labarai ta kasar waje abin da ba a saba gani ba.