Garba Shehu dan kore ne – Aisha Buhari

Aisha Buhari

Asalin hoton, @AishaMBuhari

Bayanan hoto, Aisha ta ce "Garba Shehu ba ya kare iyalan shugaban kasa yadda ya kamata"
Lokacin karatu: Minti 1

Mai dakin Shugaba Muhammadu Buhari, Aisha Buhari ta wallafa wani rubutu da yake ta karakaina a shafukan sada zumunta, inda da kanta ta caccaki mai magana da yawun Buhari, Malam Garba Shehu.

Rubutun da aka wallafa mai taken "Garba Shehu na wuce gona da iri", mai dakin Shugaba Buharin ta nuna yadda mai magana da yawun mijin nata ke 'yi wa iyalan shugaban zagon kasa'.

Aisha Buhari ta ce "Garba Shehu na daya daga cikin masu kware wa Buhari baya kasancewar yaron abokin hamayyar Buharin ne a zaben shugaban kasa, Alhaji Abubakar."

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X

Har wa yau, Aisha Buhari ta nuna rashin jin dadinta dangane da yadda Garba Shehu yaki cewa uffan a lokacin da ake yada jita-jitan auren Buhari da minista Sadiya Farouk

Aisha Buhari ta kuma zargi Garba Shehu da hannu wajen dakatar da dan jaridar gidan talabijin na NTA, Aliyu Kabir da ma'aikatar ta yi masa kan wata hira da aka yi zargin shi ya yi wa matar shugaban kasar.

To sai dai da BBC ta tuntubi Malam Garba Shehu kan batun, ya ce ba zai sa-in-sa da mai dakin mutumin da yake yi wa aiki ba.