Zazzabin Lassa ya kashe mutum 29 a Najeriya

Zazzabin Lassa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Jigawa da Kaduna da Kano da Edo da Filato da Imo da Kogi na cikin jihohin da cutar ta bulla

Mutum 29 ne suka mutu sakamakon annobar zazzabin Lassa daga cikin mutum 195 da suka kamu da cutar a Najeriya.

Marasa lafiyan da cutar ta yi ajalinsu sun rasu ne a jihohi daban-daban, yayin da kashi 89% na wadanda suka kamu da ita ke jihohin Ebonyi da Edo da Ondo.

Rahotanni daga mahukunta a jihohin sun nuna ana ta kara samun bullar cutar a jihohi.

Wuraren da aka samu bullar zazzabin na Lassa sun hada da jihohin Jigawa da Kaduna da Kano da Edo da Filato da Imo da Kogi.

Sauran su ne Abia da Bauchi da Benue da Borno da Delta da Ebonyi da Taraba da Ogun da Ondo da Osun da kuma jihar Nassarawa.

Da yake nuna damuwa kan annobar, Ministan Muhallin Najeriya Muhammad Mahmud Abubakar ya ce ma'aikatar tare da hukumar yaki da yaduwar cutuka NCDC da Hukumar Lafiya ta Duniya WHO na aiki tare domin wayar da kan jama'a a kan cutar.

Ministan ya ce hukumomin sun dukufa don ganin an dakile hanyoyin kamuwa da kuma yaduwar cutar da ake samu daga beraya.

Tana kuma yaduwa a tsakanin mutane ta hanyar ta'ammali da beraye ta hanyar taba kazantarsu ko ababen da suka taba ko wadanda suka kamu da cutar.

Hukumomin sun kafa ofisoshin tuntuba da wayar da kai kan tsaftar muhalli a jihohi, inda jami'ansu ke sa ido da bayar da rahoto kan bullar cutar ga ma'aikatar muhalli ta kasa don daukar mataki.

Ministan wanda ya jaddada muhimmancin tsaftar abinci da muhalli ya ce NCDC za ta kai aikinta na wayar da kai a kan cutar zuwa masallatai da kasuwanni da sauran wuraren haduwar jama'a.

A cewarsa ma'aikatar na bibiya domin tabbatar da ana yin aikin yadda ya kamata a dukkan matakai da kuma samar da isassun alkaluma.

Ministan ya umarci jami'an kula da muhalli a dukkan matakan gwamnati su dukufa wurin wayar da kai kan tsaftar muhalli.

Sauran matakan sun hada da gano matattarar beraye a masana'antu da kasuwanni da nufin sanya magani da kuma samar da tsaftatacciyar hanyar busar da kayan abinci da amfanin gona.

Ma'aikatun suna kuma aikin tsaftace muhalli a jihohin Edo da Ondo, ta hanyar feshin maganin kwari da raba tarkunan beraye da wayar da kan jama'a kan mahimmancin tsaftar muhalli.

Daga karshe ya shawarci jama'a da su rika kawar da abincinsu daga beraye da adana kayan abincinsu a wuraren da beraye ba za su kai garesu ba sannan su rika dafa abinci ya dahu sosai.

Sauran sun hada da zubar da shara a-kai-a-kai kuma nesa da gida da toshe kofofin da beraye ke bi da sa maganin beraye da barin cin naman bera.

Akwai kuma bukatar wanke hannu sosai da ruwa da sabulu. Su kuma ma'aikatan lafiya da ke jinyar masu cutar su rika sanya kayan kariyar fuska da na jiki.

Ya kuma yi kira ga kafafen yada labarai da sauran masu fada-a-ji su taimaka wurin yakar annobar ta hanyar wayar da kan jama'a kan hanyoyin hana kamuwa da ita.