Majalisar dokokin Iraki ta amince a kori sojojin Amurka daga kasar

Masu zaman makoki a birnin Najaf, Iraki, 4 Janairu

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Gawar Soleimani da aka yi tattaki da ita a manyan biranen Iraki ranar Asabar

'Yan majalisar dokokin Iraki sun nemi a kori sojojin Amurka daga kasar bayan harin saman da Amurkan ta kai da ya kashe janar din sojin Iran, Qassem Soleimani a birnin Baghadaza a ranar Alhamis.

Bayan kada kuri'ar amincewa da daukar matakin, 'yan majalisar sun bukaci gwamantin kasar ta mika wa Majalisar Dinkin Duniya korafi game da keta hurumi da 'yancin kasar da harin na Amurka ya yi.

Amurka ta girke sojojinta 5,000 a Iraki a wani bangare da dakarun hadin gwiwa da ke yakar kungiyar IS.

An dakatar da ayyukan rundunar ne gabanin zaman majalisar na ranar Lahadi.

Rundunar ta ce ta dakatar da ayyukanta ne domin domin ba wa sojoji damar kare sansanonin sojojin Amurka da Birtaniya da saruan kasashe a Iraki.

Kisan Soleimani ya kawo karuwar nuna wa juna yatsa tsakanin Amurka da Iran.

Karkashin jagorancin Soleimani, Iran ta ba da karin taimako ga kungiyar Hezbolla ta kasar Lebanon da sauran kungiyoyin mayakan sa kai masu goyon bayan Iran.

Iran ta kuma fadada ayyukanta na soji a Iraki da Syria inda ta ke tsara hare-haren da ake kaiwa a kan 'yan tawaye a yakin basasan Syria.

Wane tasiri kisan ke yi a Iraki?

Iraki ta tsinci kanta a cikin tsaka mai wuya a matsayin makwabciyar kuma kawar Iran mai neman daukar fansar kisan Soleimani kuma abokiyar kawancen Amurka a lokaci guda.

Gwamantin Iraki na ganin kisan Soleimani da Amurka ta yi a kasar a matsayin ya saba ka'idojin aikin dakarun kawancen.

Akwai kuma fargabar cewa 'yan kasar masu goyon bayan Iran sun ji zafin kashe Soleimani kuma akwai yiwuwar mayakan sa kai masu goyon bayan Iran na iya kai hare-haren ramuwar gayya.

Bayanan bidiyo, Cincirindon masu zuwa makokin Qasem Soleimani bayan isar gawarsa Iran

Dubban 'yan Iraki sun halarci zaman makokin Soleimani a ranar Asabar kafin a tafi da gawarsa zuwa Iran inda dubun dubatar masu juyayi suke ta yin tururuwa, gabanin jana'izarsa da za a yi ranar Talata.

Wane hukunci 'yan majalisar suka yanke?

Majalisar ta dauki matakin ba dai zama doka ba ne bayan firai ministan rikon kwarya Adel Abdul Mahdi, ya nemi kawo karshen zaman sojojin kasashen ketare a Iraki a jawabinsa ga 'yan majalisar.

Sun ce wajibi ne gwamnatin ta kawo karshen zaman sojojin kasashen waje a cikin Iraki sannan ta haramta masu yin amfani da kasarta da sararin samaniyanta da ma tekunanta.

Majalisar dokokin ta bukaci gwamantin kasar ta soke bukatarta na neman taimakon wasu kasashe a yaki da take yi da kungiyar IS, saboda "aikin sojojin ya kare a Iraki tun da an riga an samu nasara".

Gabanin kada kuri'ar da majalisar kasar ta yi firai ministan kasar ya ce ya kamata a yi gaggawan kawo karshen zaman dakarun Amurka a Iraki.

Firai minista Abdul Mahdi ya ce kawo karshen zaman sojojin Amurka a Iraki shi ne "abin da ya fi dacewa domin sake tsarawa da kuma gyara dankantaka tsakanin Amurka da sauran kasashen."

Mene ne hadarin yanayin?

Rundunar hadin gwiwar mai suna Operation Inherent Resolve, ta sanar da dakatar da ayyukata na yakar kungiyar IS domin kare kayayyakin sojojin Amurka da Birtanida da sauran kasashe da ke Iraki.

Ta buga misali da harin rokoki da ka aka kai a cikin wata biyu da uka wuce. Ana zargin kungiyar Kataib Hezbollah da ke goyon bayan Iran ce ta kai harin.

Shugaban kungiyar shi ne Abu Mahdi al-Muhandis wanda Amurka ta kashe tare da Soleimani.

"A shirye muke mu taimaka a murkushe kungiyar IS a matsayinmu na kawayen gwamantin Iraki da jama'ar Iraki da suka karbe mu hannu biyu a kasarsu," inji rundunar.

Gabanin haka Amurka ta ba wa 'yan kasarta da ke Iraki shawarar ficewa daga kasar sannan ta tura karin sojoji 3,000 zuwa gabas ta tsakiya.

Shugaba Donald Trump ya yi wa Iran kashedi cewa idan ta sake ta taba Amurkawa ko kadarorin gwamnatin Amurka to za ta dandana kudarta.

Masu sharhi na hasashen Iran za ta kai wa Amurka harin intanet ko kuma ta kai hari a kan sojojin Amurka ko wasu abubuwa masu muhimmanci ga Amurkan a gabas ta tsakiya.