Makatin da kasashen Sahel suka dauka kan ta'addanci

Hare-haren masu da'awar jihadi ta karu a baya-bayan nan a kasahen G5 Sahel na da suka hada da Nijar da Mali da Burkina Faso

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Jami'in sojin Jamhuriyar Nijar a makabartar da aka binne soja 71 da aka kashe a harin Inates

Za a tura karin dakarun soji domin yakar masu da'awar jihadi da kai hare-hare a kashe biyar na yankin Sahel.

Shugabanin Burkina Faso da Chadi da Jamhuriyar Nijar da Mali da Mauritania ne suka sanar da haka a bayan taron kwana daya na kungiyarsu ta G5 Sahel a Jamhuriyar Nijar.

Sauran matakan da shugabannin suka yi alkawarin dsauka su ne toshe hanyoyin samun kudaden shigan maharan da suka hada da safarar kwayoyi da fasakwaurin zinare.

Taron ya ce barin iyakokin kasashen sakaka babu jami'an tsaro na ba wa 'yan ta'adda damar razana al'ummomi da fadada ayyukansu a kan iyakon Mali da Burkina Faso da Nijar.

A tattaunawarsu, shugabannin G5 Sahel sun yi kira da daukar matakan soji a yankin, suna masu cewa fatara na iya sa mutane shiga kungiyoyi 'yan ta'adda.

Sun kara da cewa tsattsauran ra'ayi da ake samu a yankin na da alaka da tabarbarewar al'amuran tsaro a Libya.

Taron ya kuma yi kira ga kasashen duniya su dauki alhakin abubuwan da ke faruwa a yankin.

Shugabannin sun yi taron ne bayan wasu mahara masu ikirarin jihadi sun kashe sojan Nijar guda 71 a Inates.

Jamhuriyar Nijar na zaman makoki na kwana uku, kuma ta soke bukukuwan cikarta shekara 61 da samun 'yancin kai da aka shirya yi a ranar Laraba 18 ga wata.

Akalla sojojin Nijar da Mali da Burkina Faso guda 230 ne mahara suka kashe daga watan Satumban wannan shekara zuwa yanzu.

A 2013 Faransa ta fara girke dakarunta guda 4,500 a yankin Sahel. A watan Janairun 2020 ne shugabannin kasashen za su tattauna game cigaba da zaman sojojin Faransa a yankin.