Zaki ya kashe mutum a Nairobi

Zaki

Asalin hoton, Getty Images

Wani zaki da ya tsinke daga wurin shakatawa na kasar Kenya da ke kudu da birnin Nairobi ya sanya fargaba da zaman dar-dar a zukatan mazauna yankin.

Zakin wanda ya tsinke a ranar Litinin, ya tumurmusa wani mutum a kan hanyarsa ta shiga gari inda mutumin ya rasa ransa sakamakon raunin da zakin ya yi masa.

Hukumomi sun ce suna ci gaba da baza komar neman zakin da ya tsinke domin mayar da shi mazaunninsa.

Tuni dai aka gargadi mazauna yankin da zakin ya nufa da su zauna a gida.

Ba kasafai aka saba samun irin wannan matsala ba, inda zaki ko kuma wata dabbar daji ta kubuce daga wajen ajiye ta, ta shiga gari a Kenya.

To amma a wasu lokutan akan samu irin hakan, musamman idan dabbobin suka fusata a kan wani dalili ko kuma wasu mutane suka takura musu hakan kan harzuka su, su balle ko su fita daga inda aka kebe su su yi kan mutane.