An kama wanda ya ajiye zaki yana masa gadin gida a Legas
Jami'an hukumar kula da muhalli a birnin Lagos, sun kai samame gidan wani mutum da ya ajiye zaki a matsayin maigadinsa.
Kamar yadda rahotanni suka bayyana, jami'an sun je gidan ne a ranar Juma'a bayan mazauna unguwar sun kai korafin makwabcin nasu ya ajiye dabbar mai hadarin gaske a gidansa.
Tuni aka dauke zakin zuwa gidan adana namun daji na jihar.
Wani dan kasar Indiya ne ya ajiye zakin a gidan da yake zaman haya cikinsa.
Sai da aka harbi zakin da allurar kashe jiki kafin a samu dauke shi, a cewar wani jami'in kula da muhalli na jihar.
Tuni jami'an tsaro suka kama mutumin, domin tuhumarsa kan dalilin da ya sa zai ajiye dabba mai hadari a wurin zaman jama'a da ke unguwar Victoria Island.
"Mutumin ya yi wa mai gidan karya ne cewa zai zauna zaman haya ne a gidan, ba tare da ya ce masa zai ajiye zaki ba," a cewar jami'in LASESSO.










