Firai Ministan Malta zai yi murabus saboda kisan 'yar jarida

Joseph Muscat has been in office six years

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Joseph Muscat ya shafe shekara shida yana mulkin Malta

Firai ministan Malta Joseph Muscat ya ba da kai bori ya hau, bayan da ya yiwa al'umma alkawarin cewa zai yi murabus.

Hakan ya biyo bayan kisan wata 'yar jarida mai binciken kwakwaf a kasar Daphne Galizia.

Mista Muscat ya ce zai mika mulki a wata mai zuwa, a duk lokacin da jam'iyyarsa ta Labour ta gabatar da sabon shugaba.

A wani jawabi da ya gabatar a kafar talabijin, shugaban ya ce ya dauki alhaki kan badakalar da ba ta shafe shi ba.

To sai dai ya sha alwashin tabbatar da cewa al'amura ba su fi karfin gwamnati ba, yayin da ake zanga-zangar kira gare shi da ya yi murabus.

Kawo yanzu dai babu wanda aka gurfanar a gaban kotu da zargin kisan 'yar jaridar, duk da akwai wadanda ake zargi da hannu.