'Yan Real 12 aka gayyata tawagogin kasashensu

Real Madrid

Asalin hoton, Getty Images

Kimanin 'yan kwallo 12 na Real Madrid ne aka bai wa goron gayyata domin buga wa kasashensu tamaula a wannan makon.

A wannan lokacin babu gasar kasashe musammam a nahiyar Turai, inda za a buga karawar neman shiga gasar Turai da na kofin duniya da na sada zumunta.

'Yan wasan Real da za su buga wa kashensu karawar neman gurbin shiga gasar kofin Turai a makonnan sun hada da Sergio Ramos da Carvajal da za su yi wa Spaniya tamaula.

Tawagar Faransa kuwa ta kira Varane da kuma Areola, ita ma Belgium 'yan wasan Madrid biyu ta gayyata da ya hada da Hazard da kuma Courtois.

Gareth Bale zai yi wa Wales wasa, haka ma Croatia ta kira Luka Modric domin buga mata karawar neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Turai da za a yi a 2020.

Shi kuwa Casemiro da Militao za su buga wa Brazil wasannin sada zumunta, inda Valverde zai buga wa Uruguay tamaula sai Rodrygo da zai buga wa tawagar Brazil ta Olympic karawar sada zumunta.

Wasannin neman shiga gasar cin kofin nahiyar Turai:

Ranar Alhamis 10 ga watan Oktoba

  • Kazakstan da Cyprus
  • Belarus da Estonia
  • Netherlands da Ireland ta Arewa
  • Austria da Israel
  • Latvia da Poland
  • Arewacin Macedonia da Slovenia
  • Slovakia da Wales
  • Croatia da Hungary
  • Belgium da San Marino
  • Rasha da Scotland

Juma'a 11 ga watan Oktoba

  • Jamhuriyar Czech da Ingila
  • Iceland da France
  • Turkiya da Albania
  • Andorra da Moldova
  • Portugal da Luxembourg
  • Ukraine da Lithuania
  • Montenegro da Bulgaria

Asabar 12 Oktoba

  • Georgia da Ireland
  • Denmark da Switzerland
  • Bosnia and Herzegovina da Finland
  • Tsibirin Faroe da Romania
  • Malta da Sweden
  • Norway da Spain
  • Liechtenstein da Armenia
  • Italy da Girka

Lahadi 13 Oktoba

  • Kazakstan da Belgium
  • Cyprus da Rasha
  • Belarus da Netherlands
  • Hungary da Azerbaijan
  • Scotland da San Marino
  • Slovenia da Austria
  • Poland da Arewacin Macedonia
  • Estonia da Jamus
  • Wales da Croatia

Litinin 14 Oktoba

  • France da Turkiya
  • Moldova da Albania
  • Iceland da Andorra
  • Lithuania da Serbia
  • Bulgaria da Ingila
  • Ukraine da Portugal
  • Kosovo da Montenegro