'Yan Majalisar dokokin Najeriya za su binciki zabukan Kogi da Bayelsa

Majalisar wakilan Najeriya za tayi bincike kan zarge-zargen da aka yi game da zabukan Kogi da Bayelsa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Majalisar wakilan Najeriya za tayi bincike kan zarge-zargen da aka yi game da zabukan Kogi da Bayelsa

Majalisar wakilan Nijeriya ta umarci hadin gwiwar kwamitocinta su gudanar da bincike kan zabukan gwamna a jihohin Kogi da Bayelsa - zabukan da kungiyoyin da suka sanya ido a zaben har ma da jam'iyyar adawa ta PDP suka yi zargin an tafka magudi.

Majalisar ta ce za ta gudanar da bincike ne kan abubuwan da suka faru a zabukan da aka samu rikici da kuma zargin an yi amfani da kudi da muzgunawa masu kada kuri'a, zargin da jam'iyya mai mulki ta APC wadda ta lashe zabukan ta musanta.

Kakakin majalisar wakilai ta Najeriya Abdulrazak Namdas ya shaida wa BBC cewa za a gudanar da binciken ne ba tare da ambato sunan wata jam'iyya ba.

A cewar Namdas, an kawo kudirin da ke neman a gudanar da binciken gaban majalisar kuma aka amince da shi don a gano masu laifi da rasa rayuka yayin zabukan.

Ya ce "mun yadda an samu matsala, mun ga hotuna, mutane sun yi korafi da sauransu."

Ya kara da cewa idan har aka binciki jam'iyya, siyasa ce za ta shigo ciki kuma ba lalle a yi gaskiya a binciken ba amma "idan ka binciki wane, me ya faru? Wannan daban ne.''

Dan majalisar ya ce ba za su yi la'akari da rahoton da kungiyoyin da suka sa ido a zabukan suka gabatar ba saboda a cewar shi, makasudin yin binciken shi ne tabbatar da zarge-zargen da aka yi kan zabukan.

Duk da dan majalisar, bai bayyana wa'adin binciken kwamatocin ba, ya ce nan bada dadewa ba suke sa ran gabatar da sakamakon bincikensu domin majalisa ta san wane mataki za ta dauka akai.

A Zabukan da aka gudanar ranar 16 ga watan Nuwamba, hukumar da ke shirya zabe a Najeriyar ta ayyana gwamnan Kogi mai ci na jam'iyyar APC, Yahaya Bello amatsayin wanda yayi nasara a zaben da aka gudanar.

Baturen zaben ya sanar da cewa Yahaya Bello ya samu kuri'u 406,222, sai Musa Wada na jam'iyyar PDP ya samu kuri'u 189,704, yayin da Natasha Akpoti ta jam'iyyar SDP ta samu kuri'u 9,482.

A jihar Bayelsa kuwa, hukumar INEC ta sanar da David Lyon, dan jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben da kuri'u 352,552, kashi 25 cikin 100 na kuri'un da aka kada a kananan hukumomi takwas da ke jihar.