Majalisar Zamfara ta soke dokar biyan tsoffin gwamnoni fansho

Majalisar dokoki a jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya ta soke dokar biyan fansho ga tsoffin gwamnoni da mataimakansu.
Sanarwar da kakakin majalisar Mustapha Jafaru Kaura ya fitar, majalisar ta ce ta soke dokar kuma ya shafi tsoffin shugabannin majalisa da mataimakansu na jihar.
Kudurin dokar wanda jagoran masu rinjaye a majalisar Hon. Faruk Musa Dosara ya gabatar, ya ce tsoffin shugabannin jihar na lakumewa Zamfara naira miliyan dari bakwai duk shekara, abin da tattalin arzikinta ba zai iya dauka ba a halin yanzu.
Majalisar wadda PDP mai mulki a jihar ta mamaye ta dauki matakin ne bayan tsohon gwamnan jihar Abdul'aziz Yari Abubakar, ya nemi a biya shi kudadensa na fansho da wasu hakkokinsa.
Tsohon gwamnan wanda jam'iyyarsa ta APC ta rasa shugabanci a 2019 ya nemi a biya shi kudaden da ake biyan shi duk wata naira miliyan 10 bayan an dauki watanni ba a biya shi ba.
Tsohon gwamnan ya rubuta wa gwamnatin Zamfara wasika ne yana neman a biya shi hakkinsa, kamar yadda Mai magana da yawunsa Ibrahim Dosara ya tabbatar wa BBC.
A martanin da ta mayar, gwamnatin Matawalle ta ce wasikar tsohon gwamnan ta zo da mamaki kasancewar gwamnoni biyu da suka sauka gabaninsa ba su taba yin korafi ba.
Matakin da majalisar ta dauka yanzu na soke dokar na nufin ba za a sake biyan tsoffin shugabannin jihar makudan kudaden da suke karba ba na alawus, illa hakkokinsu da suka wajaba.











