Yadda ake fama da matsalar tituna a wasu yankunan Najeriya

Mota ba ta zuwa kauyen
Bayanan hoto, Matan kauyen sun ce ba sa iya saida amfanin gonarsu saboda rashin kyan hanya
    • Marubuci, Dooshima Abu
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Pidgin, Abuja

A lokacin da mace mai juna biyu za ta haihu, akan shiga farin ciki mara misaltuwa. Amma ga al'umar kauyen Madaka lamarin na tashin hankali, da dimuwa da bakin ciki ne idan mace za ta haihu.

Hakan na da nasaba da bakar wahalar da suke sha, sakamakon rashin kyawun hanyar da za a dauki mai nakuda zuwa asibiti. Mazauna kauyen sun ce sanadiyar rashin hanya mai kyau mata masu juna biyu da dama ne suke mutuwa akan hanya kafin a isa asibiti inda uwa da dan cikinta ke mutuwa.

Hanyar kauyen Madaka ita ce daya tilo da za ta sadaka da karamar hukumar Kagara.

Hanyar wata mahada ce ta kauyuka bakwai da suka hada da: Mgwa Magaba, da Kompani, daRubo, da Nafsira, daShikira, da Wayam, sai kuma kauyen Madaka.

Jihar Niger na daya daga cikin manyan jihohi a arewacin Najeriya, babbar binin jihar shi ne Minna, sai kuma biranen Bida da Kontagora da Suleja.

Kauyen na daga daga cikin wuraren da turawan mulkin mallaka suka zauna sakamakon arzikin danyan gwal da Allah ya yi wa yankin, amma a shekarar 1946 da farashin gwal ya fadi sai suka bar yankin.

Amma a shekarar 1976 suka sake komawa ta re da samar da jihar wadda suka bata sunan kogin Niger, haka kuma wannan jiha ita ce tushiyar biyu daga cikin shugabannin Najeriya wato Ibrahim Babangida da Abdulsalami Abubakar, dukkansu sun jagoranci kasar karkashin mulki soja.

Yawanci sun ce 'ya'yansu mata na fuskantar barazana sakamkon doguwar tafiyar da suke uyi kafin su je kasuwa
Bayanan hoto, Wata a kauyen sun ce rayuwarsu na cikin hadari sakamakon rashin kyan hanya

Hajara Kadama na daga cikin matan da jariri ya mace a cikinsu kafin akai su asibiti, ta ce lamarin ya faru ne shekara biyu da ta wuce, ta bayyana yadda abin ya faru.

" An dora ni akan babur lokacin da na fara nakuda"

"Duk lokacin da muka isa rafi, sai na sauka daga kan babur, na kwanta kan tabarma sai su sanyani cikin kwale-kwale dan haye kogin da ni",

" Sai da muka haye kogi biyar sakamakon rashin kyawun hanya, kafdin mu isa asibiti na galabaita dan haka likitoci ba su iya kubutar da jaririna ba dan ya dade da mutuwa saboda wahala."

Matasan na karbar naira 200 ga kowanne babur
Bayanan hoto, Wasu koguna sai ka biya matasa wani dan kudi kafin su ketara da abun hawanka

Tun daga wannan lokacin, Hajara ba ta sake haihuwa ba ya yin da abin ya ki bacewa daga zuciyarta.

Kogin Alhaji Bako shi ne na farko da za a fara tsallakawa kafin wasu hudu sannan a isa kauyen Madaka
Bayanan hoto, Kananan yara na wasan ninkaya a kogin Alhaji Bako

Me ya sa mata masu juna biyu ke mutuwa a cikin kogi?

Kafin a isa kauyen Madaka sai an ketara koguna hudu, sun hada da kogin Alhaji Bako, Luga, da Wayam, da Nafsira kuma dukkan kogunan ba su da gada.

Saboda rashin kyan hanyar, mota ba ta zuwa kauyen sai dai babur shi ma lokutan damuna cikin hadari hawansa ya ke.

Mata masu nakuda na ganin tasku a duk lokacin da za a kai su asbiti dan haihuwa, sakamakon bakar wahalar da suke sha daga kan babur, zuwa kwale-kwale da sauran wahalhalun da ke janyo mutuwar jariri a cikin mahaifiyarsa.

Tsahon hanyar baki daya kilo,ita 33 ne, amma ba a taba yunkurin yi m ta kwalta ba
Bayanan hoto, Hanyar kauyen Madaka kenan, a lokacin rani a lokacin damuna hanyar jagwalgwalewa ta ke yi da tabo

"Doguwar tafiyar da ake yi ke sanya matan galabaita, saboda yawancinsu kan fashe da kuka kan yadda suke jin ciwo tamkar dan cikinsu zai fasa mahaifarsu ya fito"

Wani likitan mata Dr Fred achem ya shaidawa BBC cewa "Idan an yi nasarar isa asibiti, wata sabuwar wahalar ce ke tasowa saboda idan likitoci suka bukaci ayi tiyatar gaggawa nan ma akwai hadari dan ta yiwu uwa da dan su rasa rayuwarsu sakamakon azabar da suka sha ta tsallaka koguna da kujiba-kujibar da suka shan kan babur."

Sun bukaci gwamnati ta kawo musu dauki
Bayanan hoto, Yawancin mutanen kauyen manoma ne, amma ba sa iya saida amfanin gonarsu sakamakon rashin kyan hanya

"Muna fuskantar matsaloli da hadura saboda hanyar mu ba ta da kyau, mu na ji muna gani matanmu na mutuwa tare da abin da ke cikinsu, ba ka da abin yi sai dai kuka."

"Hatta kayan amfanin yau da kullum ko na abinci ya na ma na wahalar samu, komai tsada ake saidawa a kauyen Madaka hatta gishiri tsada gare shi'', Inji Malam Aminu mazaunin kauyen Madaka.

Yini suke yi kan hanya kafin isa inda suka nufa
Bayanan hoto, Mata kan dora kayansu a kai, kafin su samu tsallaka kogin da ya hada Madaka da garin Kagara

Me gwamnati ta yi kan hakan?

Tun a shekarar 1985 ne aka yi kokarin gayara hanyar kauyen Madaka, a zamanin mulkin soja. Wani barasaken gargajiya Abdullahi Usman Kagara, ya ce zamanin mulkin soja aka fara share hanyar amma kuma ba a zuba kwalta ba kuma tun daga lokacin babu wata gwamnat da ta kawo musu daukin kammala aikin hanyar.

Amma a lokutan damuna, daga babur sai kuma dabawa a kafa idan har za a bi hanyar
Bayanan hoto, Lokacin rani ne kadai mota ke iya bin hanyar a lokacin da rafi ya ja baya

Mutanen wannan yanki, sun ce sun rubutawa gwamnati takardar korafi da rokon a gyara musu hanyar amma lamnarin ya ci tura.

Amma a lokacin rani, ana samun sassauci dan mota na bin hanyar
Bayanan hoto, a lokacin damuna ruwa kan kawo kusan wuyan masu ketarawa

BBC ta tuntubi kwamishinan ayyuka na jihar Niger, Injiniya Ibrahim Muhammad Panti, ya tabbatar da masaniya kan yadda haryar ta lalace kuma mutanen yankin manyan manoma ne da suke bukatar hanya mai kyau dan samun hanyar fitar da amfanin gona zuwa kasuwannin ciki da makoftan jihar, zai kuma yi kokarin ganin an sama musu ingantacciyar hanya.

Kafin lokacin da za a gyara hanyar kauyen Madaka da sauran garuruwa da ke kewayensa, mata irin Hajara da sauran matan kauyukan za su ci gaba da fuskantar kalubale a duk lokacin da nakuda ta kama su.

Kalubalen da hanyoyin Najeriya ke ciki

Hoton Babatunde Raji Fashola da hoton wata hanya da ta lalace a jihar Fatakwal a kudancin Najeriya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Rashin kyawun wasu hanyoyi na kara ta'azzara hadarin mota a Najeriya

Yawancin 'yan Najeriya da ministan ayyuka da gidaje Babatunde Raji Fashola na cewa ana zuzuta lalacewar hanyoyin kasar.

Ko a ranar laraba da da suke zaman tattaunawa a fadar shugaban kasa, Fashola ya ce lalacewar hanyoyin Najeriya ba ta kai yadda mutane ke fada ba.

Tun lokacin da ministan ya bayyana hakan ake suka da caccakarsa a shafukan sada zumunta inda wasu ke dauko hoton hanyoyin garinus tare da hadawa da na ministan a kokarin nuna yadda lamarin ya ke a yankunansu.

"Hanyoyin ba su yi lalacewar da ake fadi ba, na san cewa wannan maganar da na yi yawancin 'yan jarida za su dauke ta a matsayin babban labari, amma zan nanata lamarin bai kai yadda ake fada ba."

Wannan kalami bai yi wa wasu 'yan kasar dadi ba, yawanci na cewa ta yiwu ministan na zaune a wata kasar ta daban mai suna iri daya da Najeriya.