APC ta jihar Edo ta dakatar da Adams Oshiomole

Oshiomole

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Oshiomole bai ce komai ba game da dakatarwar

Gwamnonin jam'iyyar APC sun nemi shugaban jam'iyyar na kasa, Adams Oshiomole da ya yi murabus.

A wata sanarwa da darakta janar na kungiyar gwamnonin na APC, Salihu Lukman ya sa hannu, ta nemi Oshiomole da ya kira babban taron jam'iyya na kasa da gaggawa ko kuma ya fice daga jam'iyyar.

Wannan dai na zuwa ne kwana daya bayan da Jam'iyyar APC reshen jihar Edo ta dakatar da shugaban jam'iyyar na kasa Comrade Adams Oshiomole.

Shugabannin jam'iyyar na kananan hukumomi 18 a jihar ne suka kada kuri'ar yanke kauna kan Adams Oshiomole a ranar Talata, kamar yadda shugaban jam'iyyar na jihar Aslem Ojezu ya shaida wa manema labarai.

Rahotanni sun nuna cewa tsohon gwamna Oshiomole da kuma mai-ci Godwin Obaseki suna kokawar neman iko ne da jam'iyyar a jihar ta Edo.

Sai dai Oshiomole bai ce komai ba game da dakatarwar, sannan kuma babu tabbas kan yadda hakan zai shafi aikace-aikacensa a matakin kasa a matsayinsa na shugabanta.

Rikicin ya samo asali ne tun daga watan Yuni lokacin da 'yan majalisa tara cikin 24 na majalisar jihar suka zabi kakakin majalisar da sauran shugabanninta.

Za mu ci gaba da bin wannan labari domin kawo maku karin bayani da zarar mun samu.