Gebrselassie ya zargi Facebook da haddasa rikicin Habasha

Oromo

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Matasan Oromo rike da makamai a Habasha

Fitaccen dan gudun famfalaki na kasar Habasha Haile Gebrselassie ya damu kan yadda labaran karya da ake yadawa a Facebook ke taimakawa wajen rura wutar rikicin kabilanci.

Zakaran na Olympic ya shaida wa BBC cewa labaran kanzon kurege da ake yadawa a Facebook sun taka rawa a rikicin da ya faru a yankin Oromia, wanda ya jawo hararar rayuka 78.

Ya ce ya kamata a yi taka-tsantsan kada abin da ya faru a Syria da Yemen da Libya ya faru a Habasha mai mutum miliyan dari.

"Tabbas Firaministanmu yana kokarin tabbatar da zaman lafiya amma dole sai an yi aiki tare da kamfani kamar Facebook wajen tabbatar da zaman lafiya."

Ya ce yadda ake yada kalaman karya a Facebook na tattare da hatsari ga tsaron kasa.

Dan tseren gudun wanda yanzu babban dan kasuwa ne a Habasha ya yi kira ga Facebook ya taimaka ya dinga toshe kalaman karya da kan iya haifar da rikicin kabilanci da na addini.

Ko da yake ba za iya gane tasirin da kafafen sada zumunta na intanet kamar Facebook suka yi ba wajen rura wutar rikicin na watan da ya gabata, amma wasu kalaman da aka yada a Facebook suna da hatsari, musamman na karya da aka yada inda aka zargi dan sanda yana ba matasa makamai.

Rikicin Oromia ya samo asali ne bayan wani mai kamfanin jarida Jawar Mohammed ya zargi hukumomi da yi wa rayuwarsa barazana bayan janye masu gadinsa.