Turkiyya na barazanar ci gaba da luguden wuta a Syria

Turkey

Asalin hoton, Reuters

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya yi barazanar ci gaba da bude wa mayakan Kurdawa wuta muddin ba su janye daga kan iyakar Syria ba kafin yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma wa ta kare.

Shugaban ya yi gargadin cewa akwai mayakan Kurdawa kusan 1,300 da ya kamata su janye daga kan iyakar kafin karfe 22:00 (19:00 agogon GMT) na ranar Talata.

Sojojin Turkiyya da hadin gwiwar mayakan Syria a ranar 9 ga watan Octoba sun kai hari ga mayakan Kurdawa domin kafa sansani mai kusan girman kilomita 32.

Mista Erdogan ya yi alkwarin tsagaita wuta bayan bukatar da Amurka ta yi na yin hakan.

Rundunar hadin gwiwar sojoji wadanda Amurka ke jagoranta sun dogara ne da mayakan Kurdawa domin yaki da 'yan kungiyar IS kusan shekaru hudu, sai dai gwamnatin Turkiyya na daukar Kurdawan a matsayin 'yan ta'adda.

Turkiyya dai ta fara yakar mayakan Kurdawan ne tun bayan da Shugaba Trump na Amurka ya ba sojojin Amurka umarnin barin iyakar Iran - wannan wani mataki ne da 'yan majalisa a Amurka suka yi ta caccaka.

Reuters

Asalin hoton, Reuters

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa sama da mutane 176,00 ne ciki har da yara kusan 80,000 suka rasa muhallansu cikin makwanni biyu da suka gabata a arewacin Syria wanda ke da mutane kusan miliyan uku.

Wata kungiyar kare hakkin bil adama a Syria ta bayyana cewa an kashe fararen hula kusan 120 a yakin kuma an kashe mayakan Kurdawa kusan 259, haka zalika an kashe mayakan Syria da suke kawance da Turkiyya 196 an kuma kashe sojojin Turkiyya bakwai.

Jami'ai a Turkiyya sun bayyana cewa an hallaka fararen hula 20 a Turkiyyar a wani hari da mayakan Kurdawa suka kai a kasar.

A ranar Alhamis, mataimakin Shugaban Amurka Mike Pence ya shawo kan Mista Erdogan ya amince domin tsagaita wuta kan harin da yake kai wa mayakan Kurdawa na sa'o'i 120 domin bayar da dama ga Amurka ta taimaka wajen janye mayakan Kurdawan daga inda Turkiyya ke son kafa sansaninta a arewacin Syria.

Ya kuma amince da tsagaita wuta ta din-din-din bayan mayakan Kurdawan sun janye baki daya.

Mista Erdogan ya ce '' kamar yadda ministan tsaron kasata ya shaida mani, kusan mayakan Kurdawa 700 zuwa 800 sun janye, akwai sauran 12,00 zuwa 13,00 da suka rage. An ce za su janye baki daya.''

Mista Erddogan ya kuma yi gargadin cewa dole ne zuwa Talata mayakan Kurdawan su janye baki daya idan ba haka ba zai ci gaba da kai musu hari.

''Idan alkwarin da Amurka ta yi mana ba a cika shi ba, za mu dora daga inda muka tsaya, kuma a wannan lokacin za mu kara fadadashi.''