Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Hotunan gobarar tankokin mai a Onitsha
Wata tankar dakon mai ta fadi, inda ta zubar ta man a wata babbar kwata a Onitsha da ke jihar Anambra ranar Juma'a.
Wannan ya zo ne bayan wata tankar ta afka cikin kasuwar Ochanja sannan ta kama da wuta ranar Laraba a garin na Onitsha.
Mazauna unguwar Omagba Phase Two sun ce tankar ta fadi ne da misalin karfe hudu na asuba ranar Juma'a inda ta kama da wuta bayan man ya fara zubewa.
Dama dai a ranar Laraba ne wata tanka dauke da man fetur ta afka wa wasu shaguna a kasuwar Onitsha, inda man ya zube kuma shagunan suka kama da wuta. An yi asarar rayuka da kaya na miliyoyin naira.
Gobarar ta shafi shaguna a titunan Iweka da Ziks da Ozomagala.
Rahotanni sun bayyana cewa wutar na kamawa, mazauna unguwar suka tsere daga gidajensu.
Har yanzu dai ba a san adadin mutanen da suka rasa rayukansu ba a gobarar biyu, amma akwai wata mahaifiya da jaririnta da suka mutu.
Rahotanni sun bayyana cewa 'yan kwana-kwana sun gaza kashe wutar, kamar yadda a ranar Laraba ma suka gaza kashewa har sai da takwarorinsu na jihar Delta suka kai masu agaji.
Gobarar ta ranar ranar Juma'a ta shafi gidaje takwas a kan manyan titunan Okaka da Ochanja.
Kasuwar Ochanja ita ce kasuwa ta biyu mafi girma a jihar kuma tana da shaguna sama da 10,000, kuma da yawa daga shagunan sun kone.