Mayakan IS mafiya hadari da ke hannun Amurka

Mayakan Kurdawa ne suka kama wadannan mayakan na kungiyar IS

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Mayakan Kurdawa ne suka kama wadannan mayakan na kungiyar IS
Lokacin karatu: Minti 2

Biyu daga cikin kwarin IS din an fitar da su daga Siriya zuwa wani wuri wanda Amurka ke iko da shi, a cewar shuagban Amurka.

El Shafee Elsheikh da Alexanda Kotey ne aka zarga da shiga wani sashen kungiyar IS wanda ke garkuwa kuma ya kashe mutanen kasashen yamma da ke a Siriya.

Su biyun na hannun sojojin Amurka a cewar rahotannin kafafen labaran Amurka.

A wani tsokaci da shugaban Amurka ya yi a shafin Twitter, ya kira su da "Mafiya munin masu muni".

Ya bayyana cewa an fitar da su daga Siriya ne "ko da Kurdawa ko Turkiyya sun rasa iko" na wurin da ake tsare da su.

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X

A cewar jaridun New York Times da kuma Washington Post, an fitar da mutanen biyu ne daga gidan kason da mayakan Kurdawa ke iko da shi wanda yake a Arewacin Siriya.

An fitar da sanarwar ne bayan da Amurka ta kwashe sojojinta daga yankin a wannan makon.

A ranar Laraba ne Trump ya shaida wa 'yan jarida cewa Amurka ta sauya wa "mafiya hadari cikin mayakan IS" saboda tsoron da ake ji na cewa za su iya guduwa saboda wannan kutsen da Turkiyya take yi a yankunan ikon Kurdawa.

Mohammed Emwazi da Aine Davis da Alexanda Kotey da kuma El Shafee Elsheikh (daga hagu zuwa dama)

Asalin hoton, unknown/HO via Met Police, Kotey, Handout

Bayanan hoto, Mohammed Emwazi da Aine Davis da Alexanda Kotey da kuma El Shafee Elsheikh (daga hagu zuwa dama)

Kurdawa ne wadanda suka taimaka wa Amurka wajen cin galabar mayakan IS, inda suke rike da dubban mayakan tare da iyalinsu a gidajen yari. Ana fargaba kan abin da zai iya faruwa da su yanzu da yaki ya barke.

Mambobin sashen a kungiyar ta "Kwarin IS" din sun hada da Mohammed Emwazi, wanda aka fi sani da 'Jihadi John', wanda aka kashe a wani harin jirgin yaki a 2015, da Aine Davis, wanda aka daure a Turkiyya.

Rahotannin na nuna cewa mayakan kurdawa ne suka kama su a watan Janairun 2018.