Saudiyya na son Amurka ta cire Sudan daga 'yan ta'adda

Saudiyya ta ce tana kokarin ganin Amurka ta cire sunan Sudan daga jerin sunayen kasashe masu tallafa wa ta'addanci a duniya domin kasar ta ci moriyar da sauran kasashen duniya ke ci.
Saudiyya ta sanar da hakan ne a shafin Twitter bayan wata ganawa tsakanin Sarki Salman da shugaban rikon kwarya na Sudan, Laftanar Janar Abdel Fattah Abdelrahman Burhan tare da Firai ministansa Abdalla Hamdok, a birnin Riyadh.
Masarautar ta Saudiyya ta kara da cewa za ta "zuba makudan kudi kan wasu ayyukan zuba jari" da kuma "inganta wasu ayyukan da ake da su a yanzu", in ji ma'aikatar kasar waje ta kasar.
Ita ma Sudan ta yi alkawarin za ta "mara wa Saudiyya baya a tarukan kasashen duniya".
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 1

Karshen labarin da aka sa a X, 2
Kasancewar sunan Sudan a cikin jerin kasashe masu tallafa wa ta'addanci ya sa Sudan kasa samun rancen kudade daga wurare kamar Asusun Lamani na Duniya da Bankin Duniya.
Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa sun bai wa Sudan tallafin kudin da ya kai $3bn tun bayan kawar da tsohon shugaban kasar Omar al-Bashir a watan Afrilu.