'Yan sanda sun kama kayan hada bom a Abuja

Asalin hoton, NPF
Rundunar 'yan sandan babban birnin Najeriya ta ce ta kama wasu kayan hada abubuwan fashewa a Abuja.
Rundunar ta ce jami'an nata sun kama kayan ne a tashar motar Baba Nagode da ke Nyanya a wajen birnin ranar Laraba.
Wata sanarwa da kakakin rundunar 'yan sandan babban birnin tarayya DSP Anjuguri Manzah ya sanya wa hannu ta ce an kama mutum hudu da ake zargi da safarar kayan ba bisa ka'ida ba.
"Mutanen da aka kama sun hada da Hamisu Abah da Suleiman Hammeed da Onuh Sunday da kuma Agwan Bulus," in ji sanarwar.
Manzah ya ce tuni aka kaddamar da bincike kan lamarin, yana mai tabbatar wa da jama'a cewa akwai tsaro sosai a Abujar.
"A yanzu haka dai an kai wadanda ake zargin Bangaren Biciken Miyagun Laifuka na rundunar don bincikarsu.
Kuma muna kira ga al'ummar birnin tarayya da su ci gaba da gudanar da al'amuransu na yau da kullum da suka dace ba tare da wata fargaba ba, domin rundunar 'yan sandan ta sanya tsaro sosai don kare ayuka da dukiyoyinsu," a cewar Mista Manzah.







