Akwai tsaro a hanyar Kaduna- Rundunar 'yan sanda

Rashin tsaro a Abuja

Asalin hoton, Getty Images

Rundunar 'yan sanda reshen jihar Kaduna ta ce rashin tsaro a hanyar Kaduna zuwa Abuja bai dawo ba, kamar yadda wasu mutane ke cewa, bayan da aka yi garkuwa da wasu fasinjoji shidda a kan hanyar.

Jami'in hulda da jama'a na Rundunar DSP Abubakar Yakubu Sabo ya shaidawa BBC cewa "akwai isassun jami'an tsoro a hanyar, kuma duk lokacin da a ka samu wata matsala rundunar na kokarin ganin ta toshe dukkan wata kafa ta hanyar samar da ingantaccen tsaro."

DSP Sabo ya ce masu garkuwa da mutane da aka hana sukuni ne ke kawo harin gaggawa su gudu.

Wani direba da ya shaida faruwar lamarin ya bayyana wa BBC cewa 'yan bindigar sun kwashe a kalla minti goma sha biyar suna tafka ta'adin.

"Ga jami'an tsaro a hanyar amma duk da haka sai ka rasa abunda ke faruwa", a cewarsa.

Rundunar 'yan sandan jihar Kadunan dai ta tabbatar da sakin fasinjojin shidda da 'yan bindiga su ka yi garkuwa da su wanda uku daga cikin mutanen dalibai ne.

DSP Yakubu ya ce ya yi magana da shugaban sashen tsaron jami'ar da daliban su ke ya kuma tabbatar masa ba a biya wasu kudin fansa a kan su ba, amma su na ci gaba da bibiyar al'amarin.

Ya kuma ce za su fitar da karin bayani nan gaba.