Real Madrid ta ga ta leko ta koma da Valladolid

Gareth Bale

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, 'Yan Real Madrid sun ji takaicin kasa galaba a kan Real Valladolid

Real Madrid sun gamu da takaici sakamakon kwallon da Real Valladolid ta farke ana saura minti biyu a tashi wasansu na La Liga.

An dab da tashi daga karawar ne Sergio Guardiola Navarro ya samu wata dama, wadda bai yi sake ba ya garzaya ya kwarara bal din ta wuce tsakanin kafafun tsohon golan Chelsea, mai tsaron ragar Real din Thibaut Courtois.

Dan Faransa Karim Benzema ya dauka ya cika wa Real Madrid aiki da kwallon da ya ci ma ta a minti na 82, sai kwatsam labari ya sauya minti shida tsakani aka farke.

Luka Jovic wanda ya shigo daga baya ya yi kararrawa minti daya da shigowarsa filin, wanda da bai kuskure ba da ya ceci Real Madrid ta samu nasara, amma ina!

Real ta je wasan nata na biyu ne na gasar ta La Liga ta bana, bayan doke Celta Vigo 3-1 a wasanta na farko inda Gareth Bale ya sake samun damar shiga wasan tun daga farko.

Kiris dan wasan na Wales ya bar Real Madrid ya tafi China a lokacin kasuwar sayar da 'yan wasa ta baya bayan nan, amma shugaban kungiyar Florentino Perez ya dakatar da tafiyar.

Tsohon dan wasan na Tottenham ya kai hare-hare biyu, daya a kashin farko na wasan, daya kuma da ka bayan an dawo daga hutun rabin lokaci.

Valladolid ta so yi wa masu masaukin nata illa, ta kwashe makin uku gaba daya, in banda Courtois ya kade wata bal da Waldo Rubio ya sheka masa.

Teburin La Liga:

Zuwa yanzu Sevilla ce ta daya a teburin na La Liga da maki shida, da bambanci ko yawan kwallo uku a wasa biyu, Read Madrid ke bi ma ta baya da maki hudu da yawan kwallo biyu bayan wasa biyu.

Real Valladolid din ce ta uku da maki hudu ita ma da yawan kwallo daya a wasan biyu.

Sakamakon Sauran Wasannin na La Liga na mako na biyu:

Osasuna 0-0 Eibar

Celta Vigo 1-0 Valencia

Getafe 1-1 Ath Bilbao

Ci gaban Wasannin La Liga na Mako na Biyu na Lahadi da Lokacin Karawa (Agogon Najeriya):

Deportivo Alavés16 : 00 Espanyol

Mallorca16 : 00 Real Sociedad

Leganes18 : 00 Atletico Madrid

Barcelona 20 : 00 Real Betis