Trump: Ba na nuna wariyar launin fata

Asalin hoton, Getty Images
Shugaba Trump ya jaddada cewa ba ya nuna wariyar launin fata bayan da wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter mai dauke da kalaman nuna kin jini ga wasu mata hudu 'yan majalisar dokokin Amurkar suka jawo ce-ce-ku-ce.
Kalaman Mista Trump sun nuna cewa ya kamata matan hudu wadanda 'haifafun Amurka ne su bar kasar.
A wani martani da ya mayar kan sukar, Mista Trump ''Sakonnin da na wallafa ba sa nuna wariyar launin fata. Ni ba na wariyar launin fata kwata-kwata".
Kalaman nasa na zuwa ne a lokacin da majalisar dokokin Amurka ke shirye-shiryen kada kuri'a kan wani kudiri da ke allawadai da kalaman shugaban na baya.
Ana tunanin cewa za a amince da kudirin saboda jam'iyyar Democrats ita ce ke da mafi rinjayen 'yan majalisan, kuma idan 'yan jam'iyyar Republican suka goyi bayan kudirin hakan zai iya sa a amince da takardar cikin gaggawa
A baya-bayan nan 'yan majalisa Alexandria Ocasio-Cortez da Ilhan Omar da Ayanna Pressley da Rashida Tlaib sun yi watsi da kalaman nasa.
A wani taron manema labarai da aka yi ranar Litinin, sun bukaci 'yan Amurka da su yi kunnen uwar shegu da kalaman Trump.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 1
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 2
Shugaban dai bai ambaci sunayen matan ba a sakonsa na farko da ya walafa ranar Lahadi, amma akwai kwararan hujjoji da ke nuna cewa sakon na da alaka da matan wadanda aka fi sani da ''The Squad''.
Ya janyo ce-ce ku-ce bayan da ya ce "matan asalinsu 'yan wasu kasashe ne da gwamnatocinsu ba su da tsari kwata-kwata" kuma ya kamata su tafi gida.
Uku daga cikin matan dai a Amurka aka haifesu, daya kuma Ilhan Omar, haifaffiyar Somaliya ce amma ta zo Amurka lokacin da take yarinya.
Bayan da wannan lamarin ya faru, 'yan majalisar hudu sun shaidawa manema labarai cewa suna so su kara mayar da hankali kan manufofin shugaban.
Ilhan Omar ta ce sukarsu da Mr Trump yayi yana cike da nuna yadda ya ke nuna wariyar launin fata kan matan hudu kuma ta ce wannan nuna tsananin kishin farar fata ne.
Ta kuma kara da cewa, shugaban na so ne kawai "ya raba kasarmu."
Rashida Tlaib ta kira wannan yunkurin wani ci gaba na abubuwan da ya saba yi na nuna wariyar launin fatan.











